United na son Baleba, Arsenal na harin Konsa da Guimaraes

Carlos Baleba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Carlos Baleba
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Bayan gazawa wajen siyen Mateus Fernandes, Manchester United, a shirye suke wajen taya an wasan Brigton da KamaruCarlos Baleba. (Give Me Sport).

Har yanzu Arsenal ba su fidda ran ɗaukar ɗan wasan Newcastle Bruno Guimaraes, inda suke shirye-shiryen taya shi kan fam miliyan 60. (Sun)

Yayin da Barcelona da Atletico Madrid, ke son ɗaukar dan wasan ArjentinaJulian Alvarez, su na kuma sa ido kan tsohon ɗan wasan Machester United Mason Greenwood, wanda yanzu ya ke taka leda a Marseille. (Sport - in Spanish)

Mai tsaron raga Arsenal Kepa Arrizabalaga ya sanar da ƙungiyar cewar zai tafi a ƙarshen kakar nan, inda tsohon mai tsaron ragar Leeds United Illan Meslier, ke cikin waɗan da ake sa ran zasu maye gurbinsa. (Teamtalk)

Arsenal na harin ɗan wasan Ingila da Aston Villa Ezri Konsa a wannan kaka. (Telegraph)

Ɗan wasan Aston Villa da Ingila Ollie Watkins ya zama ɗan wasan da kowa ke mamaki cewar Fenerbahce ke nema. (Sun)

Leeds United ta amince da farshin fam miliyan 23 da kan ɗan wasan Southampton Shea Charles, bayan da aka da ƙi amincewa da tayinsu, na farko kan ɗan wasan. (Mail)

Ac Milan na duba yiwuwar siyar da ɗan wasan Ingila Fikayo Tomor, a wannan kaka yayin da ya ke shekarar ƙarshe na kwantarginsa da ita. (Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan Roma da Morrocow Neil El Aynaoui na cikin ƴan wasan da ƙungiyoyin da ke Ingila irin su Manchester United, da Liverpool, da Chelsea, da Aston Villa, da Brighton, da Bournemouth, sai Newcastle United da Sunderland na zawarcin ɗan wasan. (Teamtalk)

Everton ce ƙungiyaoyi na baya-bayan nan da ke buga gasar Firimiya, da ake alƙantasu da ɗan wasan Benfica da Colombia Richard Rios. (Sport Witness)