Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai faru tsakanin Bayern da Arsenal, Real da Leipzig?
Za a ci gaba da wasa na uku-uku a cikin rukuni a Champions League, inda za a yi fafatawa 9 a manyan filayen da ke nahiyar Turai.
Daga cikin karawar da za ta ja hankali ta hada da wasan Bayern Munich da Arsenal da wanda RB Leipzig za ta ziyarci Real Madrid a Santiago Bernabeu.
Jerin wasannin da za a buga ranar Laraba:
- Como vs Manchester United
- Lille vs Galatasaray
- Aston Villa vs Viking
- Club Brugge vs Lens
- Bayern München vs Arsenal
- Inter vs Shakhtar Donetsk
- Real Madrid vs Leipzig
- Real Betis vs Feyenoord
- Sporting CP vs LASK
Bayern Munich da Arsenal
Bayern Munich za ta karbi bakuncin Arsenal a Allianze Arena a wasa na uku-uku a cikin rukuni a gasar ta Champions League ranar Laraba.
A wasanta na farko a gasar Champions Leagu na wannan kaka Arsenal ta bi Napoli har gida ta doke ta da ci ɗaya, inda aka tashi Napoli 0-1 Arsenal, kuma ta doke Lille da ci uku a Emirate a wasa na biyu (Arsenal 3-0 Lille).
Ita kuwa Bayern Munich ta lallasa Bodo/Glimpt da ci biyar (Bayern 5-0 Bodo/Glimp) a wasan farko na gasar a wannan kaka, amma ta yi canjaras ne da Viking a wasa na biyu inda aka tashi Viking 3-3 Bayern Munich.
Bayern Munich ta yi nasara a wasanni takwas cikin karo 15 da kungiyoyin suka kara a gasar ta zakarun Turai, Arsenal ta ci wasa hudu da canjaras uku a tsakaninsu.
Dan wasan Bayern Munich, Serge Gnabry ya fara ne daga makarantar matasa ta Arsenal, inda ya buga wasa 15 tsakanin shekarun 2012 zuwa 2014.
Harry Kane ya fuskanci Arsenal sau 22 a dukkan fafatawa, yayin da yake taka leda a Tottenham da Bayern Munich, inda ya zura ƙwallo 15 a waɗannan wasannin.
Dan wasan tawagar Ingila ya buga wasa da Arsenal a kowace kakar daga 2014/15 zuwa 2023/24, kuma ya zura a ƙalla ƙwallo ɗaya a ragar su a dukkan waɗannan kaka goma. Haka kuma ya ci ƙwallo a wasa tara a jere da ya buga a Gasar Zakarun Turai.
Bayern ba ta yi rashin nasara ba a wasa 39 a gida da ta buga a matakin rukuni, inda ta yi nasara 37 sannan ta yi canjaras biyu.
Sai dai rashin nasarar gida ta ƙarshe da ta yi a wannan mataki shi ne a hannun Manchester City da ta ci 3-2 a watan Disamban 2013.
Bayern ta zura ƙwallo a kowanne wasa cikin 23 na baya bayan nan da ta buga a Gasar Zakarun Turai, yayin da wasa takwas da ta yi a gasar aka ci jimillar ƙwallao 44, wanda ke nufin matsakaicin 5.5 a raga a kowane wasa.
Arsenal ta samu nasara sau ɗaya kacal cikin wasanni takwas na ƙarshe da ta buga a Turai a ƙasar Jamus, inda ta yi canjaras biyu kuma ta sha kashi biyar.
Gunners ta yi nasara a wasa 14 na baya bayan nan da ta buga a matakin gasar ta Gasar Zakarun Turai, kuma bakwai daga cikin waɗannan nasarorin ta samu su ne a waje da gida.
Yaya tarihin wasan Real Madrid da RB Leipzig?
RB Leipzig ta ziyarci Real Madrid a wasa na uku a cikin rukuni a gasar Zakarun Turai da za a fafata a Santiago Bernabeu.
Real Madrid ta doke Inter Milan a wasan Champions League na farko a wannan kaka (Real Madrd 2-1 Inter) sannan ta doke Roma a wasa na biyu (Roma 3-4 Real Madrid).
Ita kuma Leipzig ta sha kashi ne a hannun Como (4-0) a wasan farko da ta buga a gasar, kafin ta yi nasara kan PSV (1-0) a wasanta na biyu.
Waɗannan ƙungiyoyin sun haɗu sau huɗu a Gasar Zakarun Turai. A matakin rukuni a kakar 2022/23, Real Madrid ta yi nasara da ci 2-0 a gida sannan ta sha kashi 3-2 a hannun RB Leipzig a Jamus.
A zagayen kungiyoyi 16 a kakar 2023/24 kuwa, Real Madrid ta yi nasara da ci 1-0 a Leipzig sannan ta yi kunnen doki 1-1 a Madrid.
Yan Diomande ya koma Real Madrid daga RB Leipzig a watan Agusta kan kwantiragin shekara bakwai, bayan ya ci ƙwallo 13 a wasa 36 da ya buga a kakarsa guda ɗaya tare da ƙungiyar ta Jamus.
Dan wasan Madrid, Ibrahima Konate ya buga Leipzig wasa 66 tsakanin shekarun 2017 zura 2021.
Madrid ta zura ƙwallo a kowanne wasa cikin 26 da ta buga a gida a Turai da ƙungiyoyin Jamus, haka kuma ta ci ƙwallo a karawa 44 da ta yi a gida a Gasar Zakarun Turai.
Kylian Mbappé ya zura ƙwallo a wasa huɗu da ya yi a Gasar Zakarun Turai, sannan ya ci wa Paris Saint-Germain ƙwallo a karawar da suka yi da Leipzig a matakin rukuni a watan Oktoban 2021.
Vinícius Júnior ya zura ƙwallo biyu a ragar Leipzig a Gasar Zakarun Turai yayin da yake taka leda a Madrid, wato ya ci ɗaya a wasan da suka sha kashi 3-2 a wajen gida a watan Oktoban 2022 da kuma daya a wasan kunnen doki 1-1 a gida a watan Maris na 2024.
Denzel Dumfries yana bukatar wasa ɗaya, domin ya kai karawa 50 a Gasar Zakarun Turai.
Leipzig ta yi rashin nasara a wasa shida da ta buga a waje a matakin rukuni a sabon tsarin gasar ta Gasar Zakarun Turai.
Christopher Nkunku mai ƙwallaye 11 ya yi kan-kan-kan da Emil Forsberg a matsayin wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a Leipzig a Gasar Zakarun Turai.
Nkunku ya zura ƙwallo a wasan da Leipzig ta doke Real Madrid da ci 3-2 a gida a matakin rukuni a watan Oktoban 2022.