Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko me yasa ƴan adawa ke tayar da jijiyoyin wuya kan alƙawarin yin wa'adi ɗaya na Peter Obi?
Jam'iyyu a Najeriya na ci gaba da mayar da martani kan kalaman tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, cewa yana nan daram kan matsayarsa ta yin wa'adi ɗaya kacal idan har ya zama shugaban ƙasa, ko da kuwa an sa masa bindiga a ka.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na News Central, inda ya ce tabbatar da daidaito da mutunta tsarin rabon mulki tsakanin yankunan ƙasar ne suka sa ya ɗauki wannan matsaya.
Sai dai jam'iyyun hamayyar ƙasar sun yi watsi da kalaman nasa, inda suka bayyana su a matsayin na yaudara da neman jan hankalin jama'a.
A cewar jam'iyyun hammayar ƙasar ba wannan ne karon farko da Peter Obi ke yin alƙawari ba , sa'anan daga bisani a ga ya saɓa.
Dan haka ba bu wani dalili da zai sa al'umma su ɗauki batun da muhimanci.
Malam Bala Ibrahim shi ne kakakin jam'iyyar APC mai mulki kuma ya shaidawa BBC cewa ba su ga wani dalili da zai sa mutane su ɗauki maganarsa da muhimancin ba.
''Kamata ya yi mutane su ɗau wannan magana tasa, su jinjinata su duba ta ,su yi amfani da hankali wajan yin aiki da ita''
''Alƙawari ne wanda ina tabbatar ma ka ba zai cika ba'' in ji shi
Wasu dai na ganin cewa alƙawarin Peter Obi wani sabon salo ne da ya ke son ya kawo cikin tsarin siyasar ƙasar, sai dai Malam Bala Ibrahim ya ce kundin tsarin mulki ya fi komai kuma wasu za su iya amfani da shi a matsayin hujja domin shawo kansa nan gaba idan ya hau mulki.
''Wasu ne za su zo ma sa da hujja cewa kundin tsarin mulki ya ba shi ƴancin ya tsaya sau biyu, don me ya sa zai ce zai yi dogaro da wani alƙawari da ya yi''
''Alƙawarinsa, ƙasa ya ke da tanadin da kundin tsarin mulki ya yi, faɗa ce kawai, dan alƙawari ne wanda ya san ba zai cika ba'' in ji shi.
Jam'iyyar APC ta ce haƙƙi ya rataya akanta ta sanar da mutane, ta ɗorasu a kan turba ta gaskiya idan suka ga cewa za a yi mu su coge , domin kauce wa zaɓen tumin dare.
Ita ma jam'iyyar hammaya ta ADC ta bakin mai magana da yawunta Faisal Kabir ta nuna shakku kan kalaman Mista Obi.
''Ba ya buƙatar sai an sa mai bindiga, mutum ne wanda kowa ya san shi, ba ya cika alƙawari, da ace mutum ne mai cika alƙawari ne ya faɗi wannan magana, to ko shaka ba za a yi mamaki ba''
''Ba bu wani irin gata da APC ba ta yi mi shi ba amma ya yaudareta ya fita, dan haka duk abinda zai faɗa ma domin kowa yanzu ya san waye shi, ya san me ye halinsa'' in ji shi.
Sai dai Ibrahim Huseini Abdulkarin na hannun daman Peter Obi ya kare abinda ya faɗa.
''An riga an saba da duk ɗan siyasa maƙaryaci ne , duk ɗan siyasa ɗan yaudara ne, kuma ana son dukanmu ƴan arewa da kuma ƴan Najeriya ga baki ɗaya mu amince cewa shugabbanin mu ba su da mutunci, ba su da gaskiya kuma ba za su taɓa yin gaskiyaba''
''Mu a wannan tsari da tafiya da mu ke muna ganin ba haka ya kamata a ci gaba ba kuma waɗanda suke ta hammaya su na ganin abinda ya ke faɗi ba daidai ba ne saboda su ma su na ganin su na faɗawa mutane abinda ba daidai ba''
''Abu ne da muka tabbatar da cewa zai iya zartar da shi tun da mun ga abubuwa daya wa, waɗanda ya yi alƙawari kuma ya tabbatar ya cika'', in ji shi
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun rarrabuwar kawuna da rikice rikicen cikin gida a cikin jam'iyyun ƙasar yayinda zaƙen ƙasar ke ƙara matsowa kusa
A baya baya nan ne tsohon gwamnan Jihar Anambra Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka sauya sheka daga jam'iyyar ADC zuwa NDC.
Jam'iyyar ta NDC ta sanar da mika tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2027 ga shiyar Kudancin ƙasar.