Yaran da aka haifa kusa da sansanin sojin Birtaniya a Kenya sun gano gaskiya kan mahaifansu

- Marubuci, Josephine Casserly
- Marubuci, Ivana Davidovic
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
"Edward", ɗan shekara tara daga Kenya, ya kasance yana da matsaniyar cewa mahaifinsa ya yi aiki da sojojin Birtaniya. Launin fatarsa da ya kasance fari sabanin sa'o'insa ya janyo masa tsangwama na tsawon shekaru.
Mahaifin Edward (wanda ba asalin sunansa ba) ya ɓace tun kafin a haife shi, lamarin da ya bar mahaifiyarsa cikin tsananin talauci, inda wasu ƴan uwa suka mayar da ita saniyar ware.
Yanzu dai wannan mutumin, wanda ya yi aiki a matsayin soja ɗan kwangila a sansanin sojojin Birtaniya da ke Kenya, tare da wasu 19 da suka yi aikin soja a can, an gano su ta hanyar gwajin kwayar haihuwa, kuma a matsayin iyayen yaran da aka haifa a kusa da sansanin.
Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da mutum 12 waɗanda suka haifi yara a kusa da sansanin wanda alkalin kotun kolin iyali na Birtaniya ya yi.
Lamarin ya amsa tambayoyin ɗimbin yara waɗanda ba su san su waye ne iyayensu ba.
Duka yaran sun fuskanci wahalhalu na kuɗi da kuma kokarin gano asalinsu. Mutum 12 da aka tabbatar da iyayensu a yanzu suna da damar samun ƴancin zama ƴan Birtaniya. Wadanda suke kasa da shekara 18 ko kuma kuma ke karaty, za su samu damar tallafi.
Wani lauya a Birtaniya James Netto da kuma wani Kelvin Kubai a Kenya, sun ce akwai kusan yara 100 da aka haifa kusa da sansanin sojin Birtaniya a Kenya. Netto ya ce alkaluman za su iya fin haka.

Sansanin Batuk wanda aka kafa a shekara ta 1964 kuma wanda ke yaye sojoji Birtaniya sama da 5,000 a kowace shekara, ya yi ta janyo cece-kuce a tsawon shekaru da aka kafa shi a yankin Nanyuki, wata kasuwa mai nisan kilomita 185 da arewacin Nairobi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani rahoton bincike da majalisar dokokin Kenya ta wallafa a watan Disambar 2025, ya zargi sojojin Birtaniya da rashin hukunta waɗanda suka aikata laifi a sansaninc, abin da ya kai ga samun laifukan cin zarafin jima'i, zargin kisan gilla biyu, take ƴancin ɗan'adam, lalata muhalli da kuma watsi da yara.
Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta mayar da martanin cewa "tana nuna matukar taƙaici ga abubuwan da suka faru sakamakon kasancewar dakarun ƙasar a Kenya... Za mu ci gaba da ɗaukar matakin da ya dace domin shawo kan matsalolin".
An fara sanar da James Netto lamarin yaran da ke neman mahaifansu a yankin Nanyuki a 2024. Ya haɗa kai da wani ƙwararre kan haihuwa farfesa Denise kafin su kai ziyara zuwa Kenya.
Daga nan suka fara bincike ta hanyar gwaje-gwaje domin gano iyayen yaran waɗanda suka kasance sojojin Birtaniya - shekarun yaran ya kama daga uku zuwa 70.
"Ban taɓa ganin abu irin wannan ba, inda ake gwajin kwayar haihuwa da yawa a kotunan Birtaniya, in ji Netto.
Ya ce sun ji daɗi da sakamakon da suka samu daga binciken. "Mun samu wasu iyalai suna nesa wasu kuma a kusa, kuma an yi haka ne duka don gano iyayen yaran."
Sakamakon binciken ya zama abin farin ciki ga Edward da mahaifyarsa Nasibo, saboda yanzu zai samu tallafin kuɗi a madadin mahaifinsa.

"Na kasance ina tunanin cewa sojojin Birtaniya mutanen kirkiri ne," in ji Nasibo. Ta yi imanin cewa mahaifin Edward ya so ta da gaske da kuma kula da ita. Mun ga wata wasika da mahaifiyar sojan ta aika wa Nasibo, kafinta samu juna biyu, inda ta gode mata saboda sanya ɗanta farin ciki.
Lokacin da Nasibo ta faɗa masa tana da juna biyu, ta ce ta ji farin ciki sosai. Ya faɗa mata cewa ta saka wa yaron sunan yayansa idan ya kasance namiji, in ji Nasibo, sannan ya koma Birtaniya.
Sai dai, lokacin da juna biyun Nasibo ya kai wata huɗu, ta ce mijin ya faɗa mata cewa zai koma Birtaniya saboda wani aikin gaggawa.
Wasu ƴan uwan Nasibo sun tilasta mata barin gidan da take ciki, in ji ta, kuma an yi ta tsangwamar ɗanta a makaranta saboda launin fatarsa da ya kasance fari.
"Sun saka masa sunan 'ɗan mulkin mallaka daga Birtaniya'," kamar yadda mahaifiyar ta faɗa mana. Birtaniya ce ta yi wa Kenya mulkin mallaka daga 1895 zuwa 1963
Netto ya samu damar gano mahaifin Edward bayan da kotu ta umarci ma'aikatar tsaro da sashen ayyuka da fansho su ba da bayanan sunansa da kuma adireshi. Mutumin ya buƙaci Netto kada ya faɗa wa Nasibo ko kuma ɗansa bayanansa, sai dai lauyan yana kokarin shigar da kara don tilasta sojan biyan kuɗin renon yaro.
Ita ma, wata ƴar Kenya mai shekara 18 Yvonne, ba ta ma san komai dangane da mahaifinta ba, ba kamar Edward ba. An faɗa mata cewa ya yi aiki da sojojin Birtaniya amma ba ta san sunansa ba, inda ta tashi da sanin cewa ya mutu. Mahaifiyarta ta mutu tun tana karama, sannan sojoji a sansanin Batuk sun faɗa wa kakanninta cewa mahaifinta ya mutu.
Bincike da aka yi ya gano cewa mahaifin yarinyar yana raye, kuma har ya samu halartar kotu ranar da aka fara shari'arsa. A yanzu ba ya son haɗuwa da Yvonne. Sai dai ɗan uwan mahaifyarsa ta ce ta zaƙu ta ga Yvonne.

Netto da Kubai na ci gaba da aikinsu kamar yanda suka bayyana, inda ake kokarin shigar da ƙarin kararraki kan lamarin a gaban babban kotu a Birtaniya a cikin watanni masu zuwa.
Binciken da majalisar dokokin Kenya ta yi a watan Disamba kan lamarin, ya yi kira ga gwamnatin Nairobi da ta samar da sabbin tsare-tsare "don tilastawa sojojin Birtaniya kula da yaran da aka haifa ba tare da aure ba, ciki har da yin gwaje-gwajen kwayoyin haihuwa".











