Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool na harin Read, yayin da Gabriel ke son barin United
Liverpool na ci gaba da sa ido kan ɗan wasan Feyenoord Givairo Read, sai dai Manchester City da Arsenal su ma na harin ɗan wasan. (Teamtalk)
Yadda Manchester United ke ci gaba da funskantar koma baya ne, ya sa JJ Gabriel ke son barin Old Trafford. (Mail)
Jami'ai a Manchester United sun yi mamakin gani hannun babban wakilan ɗan wasa JJ Gabriel, Ali Barat kan gaba nemar wa ɗan wasan makomar bayan da ya shirya wata ganawa da Real Madrid da Bayern Munich a madadin ɗan wasan da iyalansa. (Express)
Ɗan wasan Brazil Raphinha, zai ci gaba da zama a Barcelona, kuma tuni aka yi zaman farko kan sabunta kwantarangin na sa, inda tsohon kwantaragin nasa zai ƙare a 2028. (AS - in Spanish)
Tottenham ba za ta ɗauki ɗan wasan Ajantina Mauro Icardi ba, da zai zama mai zaman kansa a kakar siyen ƴan wasa. (Football Insider)
Brighton & Hove Albion da Aston Villa na son ɗaukar ɗan wasan Nacional Mauro Coronel. (Teamtalk)
Newcastle na harin matsan ƴan wasan tsakiya da na gefe, a kakar siyen ƴan wasan a watan Janairu, da ma bayan nan. (The I)
Barcelona ta shirya sanya fam miliyan 428, kafin ta saki ɗan wasan Sipaniya Marc Bernal. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Ɗan wasan gaban Liverpool Florian Wirtz, na iya zama cikin ƴan wasan da zai iya komawa Bayern Munich, idan har suka cimma matsaya da ƙungiyar, nan gaba.(Football Insider)