Gwamnan jihar Pennsylvania, Tom Wolf, ya bayyana cewa ba lallai a samu sakamakon jihar ba a yau, a zaben shugaban ƙasar da aka gudanar.
"Ba lallai a samu
sakamakon zaɓen ba a yau, sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne za a samu
sakamako mai inganci, ko da sakamakon ya ɗauki lokaci bai fito ba," kamar
yadda ya shaida wa manema labarai.
Sakataren harkokin
wajen jihar Kathy Boockvar, ya ce kusan kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka
jefa ta akwatin gidan waya an ƙirga su, inda ya ƙara da cewa wannan ne zaɓe
mafi inganci da ya taɓa gani.
Mista Trump ya bayyana
cewa "abu ne mai wuya" Biden ya kamo shi a yawan ƙuri'u a
Pennsylvania, wadda ita ce jihar da ya samu nasara da ƙuri'u 44,000 a 2016.
Jihar
na da kwamitocin masu zaɓen shugaban ƙasa 20.