Farfesa Umar Danbatta, shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya Nigerian Communications Commission (NCC), ya ce masu amfani da layin wayar salula a Najeriya sun ƙaru zuwa milyan 199.3.
An samu ƙaruwar ne daga miliyan 184 a watan Disamban 2019 zuwa Mayun 2020.
Dambatta ya bayyana haka ne yayin miƙa lamunin kuɗi da NCC ta bai wa wasu cibiyoyin sadarwa biyu da za su gudanar da bincike kan annobar korona ranar Talata, wanda ya gudana ta intanet.
Ya ƙara da cewa masu amfani da intanet ma sun ƙaru a tsawon wannan lokacin daga miliyan 126 zuwa 147.1, yayin da masu sayen layin intanet a dunƙule wato broadband suka ƙaru daga miliyan 72 zuwa 80.2.
Kasancewar Najeriya na da al'umma kusan miliyan 200, hakan na nuna cewa kashi biyu cikin uku na 'yan ƙasar na amfani da intanet.
"Irin waɗannan [bincike] za su taimaka wurin samar da yiwuwar gudanar da taruka ta intanet da za su riƙa samar da tazara [tsakanin mutane]," in ji shi.