Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 24/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 24/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Ebola ta kashe mutum fiye da 200 a larduna biyu na DR Kongo'

    Jami'an lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo sun ce cutar Ebolar da ta ɓarka a yanzu ta haddasa mutuwar mutane fiye da 200 a larduna biyu.

    Haka kuma adadin waɗanda suka kamu da cutar ya ƙaru zuwa mutum fiye da 860.

    Akwai damuwar da ake da ita cewa jami'an lafiya da kuma ma'aikatarn agaji ba sa iya kai wa ga mutanen da cutar ta shafa bayan da 'yan tawayen M23, suka rufe babban filin jirgin saman da ke Goma, wato inda suke ajiye makamansu, lamarin da ya tursasawa ƙungiyoyi agaji komawa shiga ta yankin Kivu.

    Cutar Ebolar - da ta barke a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo - ita ce mafi muni da ta barke a Afirka da ba a taɓa ganin irinta ba a tsawon shekara 10.

    A jiya Asabar ne, gwamnatin ƙasar ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a birnin Bunia da ke arewa maso gabashin ƙasar domin takaita haɗarin yaɗuwar cutar.

  2. An cimma matsayar kawo ƙashen yaƙin Iran - Trump

    Shugaba Trump na Amurka ya ce an cimma matsaya a kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ƙasarsa ke yi da Iran.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce ya bayyana matakin ne bayan wayar da ya yi da shugabannin ƙasashen Larabawa a karo daban-daban da kuma Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

    Shugaban na Amurka ya ce cikin yarjejeniyar da aka cimma akwai batun sake buɗe mashigar Hormuz.

    Ya ce yanzu ana tattauna matakin ƙarshe na yarjejeniyar kuma nan ba da jimawa ba za a sanar da abin da aka cimma.

    To sai dai kafar yaɗa labaran Iran ta Fars, mai kusanci da dakarun juyin juya halin Iran, ta ce mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin ikon Iran.

  3. Wani ɗan bindiga ya buɗe wuta a kusa da fadar gwamnatin Amurka

    Jami'an tsaro na sirri sun tabbatar da kisan wani ɗan bindiga da ake zargin ya buɗe wuta a kusa da fadar gwamnatin Amurka ta White House, bayan da suka yi musayar wuta da jamian tsaro na farin kaya.

    Jami'an sun ce mutumin da ake zargi sai da ya tunkari wani wajen binciken ababan hawa da ke kusa da ginin sannan ya buɗe wuta a kan jami'an tsaron da ke wajen.

    Ba tare da ɓata lokaci ba jami'an tsaron suka mayar masa da martani inda aka ji masa rauni shi da wani mutum da ke kusa da shi.

    An dai kai mutumin da ake zargi asibiti inda daga bisani kuma ya mutu. Lokacin da aka kai harin shugaba Trump na cikin fadar ta white house.

  4. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa