'Ebola ta kashe mutum fiye da 200 a larduna biyu na DR Kongo'

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo sun ce cutar Ebolar da ta ɓarka a yanzu ta haddasa mutuwar mutane fiye da 200 a larduna biyu.
Haka kuma adadin waɗanda suka kamu da cutar ya ƙaru zuwa mutum fiye da 860.
Akwai damuwar da ake da ita cewa jami'an lafiya da kuma ma'aikatarn agaji ba sa iya kai wa ga mutanen da cutar ta shafa bayan da 'yan tawayen M23, suka rufe babban filin jirgin saman da ke Goma, wato inda suke ajiye makamansu, lamarin da ya tursasawa ƙungiyoyi agaji komawa shiga ta yankin Kivu.
Cutar Ebolar - da ta barke a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo - ita ce mafi muni da ta barke a Afirka da ba a taɓa ganin irinta ba a tsawon shekara 10.
A jiya Asabar ne, gwamnatin ƙasar ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a birnin Bunia da ke arewa maso gabashin ƙasar domin takaita haɗarin yaɗuwar cutar.














