Shugaban Kamaru Paul Biya, wanda shi ne mafi tsufa a duniya - kuma wanda ya bar ƙasar sama da kwana 40 da suka gabata - ya amince da karɓo bashi domin aiwatar da kwangiloli.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsawon lokacin da ya kwashe ba tare da dawowa ƙasar ba.
A wasu matakai daban-daban da ya ɗauka a ranar Laraba, shugaban mai shekara 93 ya buƙaci ministan tattalin arziki da ci gaban yankunan ƙasar ya sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin karɓar bashi daga ƙungiyar ci gaban ƙasashen duniya (IDA) da kuma Bankin Deutsche na Spaniya.
Haka nan kuma shugaban ya naɗa wasu jami'ai biyu na hukumar kula da harkar man fetur da iskar gasa ta ƙasar duk a ranar guda.
Sai dai kasancewar babu wanda ya sanya ido kan shugaban ƙasar tun daga ranar 7 ga watan Yuni, matakan da aka ce shugaban ya ɗauka sun tayar da ƙura, inda mutane da dama a ƙasar ke neman sanin inda shugaban yake da kuma gaskiyar bayani game da lafiyarsa.
Sai dai na kusa da Biya sun bayyana tafiyar tasa zuwa ƙasashen waje a matsayin "taƙaitaccen hutu na ƙashin kai a nahiyar Turai", to sai dai daɗewar tasa ba tare da an gan shi ba na ci gaba da haifar da muhawara tsakanin al'ummar ƙasar.
Lamarin ya haifar da raɗe-radi game da lafiyar shugaban ƙasar - wani abu da ba kasafai aka cika tattaunawa kansa ba a bayyane, a ƙasar, wadda Biya ya kwashe shekara 44 yana mulka.
A ranar 17 ga watan Yuni, mujallar Jeune Afrique ta ruwaito cewa an kwantar da Paul Biya a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Geneva na ƙasar Switzerland bayan fama da wani zazzaɓi jim kadan bayan bikin zagayowar ranar ƴancin kan ƙasar a watan Mayu.
Sai dai ministan yaɗa labarai na ƙasar Rene Emmanuel Sadi ya fito nan take ya ƙaryata rahoton a wata sanarwa da ya fitar washegari, inda ya bayyana labarin a matsayin maras tushe.
Duk da cewa Sadi ya tabbatar da cewa Paul Biya yana birnin Geneva, amma ya ƙaryata batun cewa an kai shugaban ƙasar asibiti, kuma sannan babu wata matsala a game da lafiyarsa kamar yadda mujallar ta ruwaito.
"Duk da cewa shugaban ƙasar zai iya yin amfani da damarsa a lokacin da yake hutu a Geneva domin ganin likita a duba lafiyarsa kamar yadda ya saba, amma yana ci gaba da lura da al'amuran ƙasar yadda ya kamata kuma yana ɗaukar matakan da suka dace a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ya bayyana.
Rashin ganin nasa na tsawon lokaci ya janyo martani daga jam'iyun adawa, inda wani ɗan majalisar dokokin ƙasar ya buƙaci majalisar tsarin mulkin ƙasar ta yi amfani da ƙarfinta wajen sauke shugaban ƙasar.
Sai dai a martanin da ta mayar, jam'iyyar CPDM mai mulkin ƙasar ta yi watsi da batun, tare da cewa shugaban na kan muƙaminsa daram, sannan ta ƙara da cewa duk wani kalami irin hakan tamkar ƙirkirar doka ce da ba ta wanzuwa.
"Babu wata doka ko tanadi a Kamaru da ya ƙayyade iyakar lokacin da shugaban ƙasa zai iya kwashewa ba ya ƙasar," in ji mai magana da yawun gwamnati a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya jaddada cewa Biya na ci gaba da aiki daga inda yake.
A dokokin Kamaru, za a iya ayyana gurbi a muƙamin shugaban ƙasa ne kawai idan shugaban ya ajiye aiki don raɗin kansa, ko ya mutu ko kuma majalisar kundin tsarin mulki ta ayyana shi a matsayin wanda ba zai iya gudanar da ayyukan da suka rataya a kansa ba.
Rashin ganin Biya na ƙara tayar da ƙura ne kasancewar hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake muhawara kan naɗa mataimakin shugaban ƙasar da kuma yin garanbawul ga majalisar zartarwa, wanda masharhanta ke ganin cewa har ma an makara.
A tsawon mulkinsa, wanda ya fara tun a shekarar 1982, shugaban na Kamaru yakan yi tafiye-tafiye akai-akai da kwashe lokuta masu tsawo a ƙasashen turai, inda sau da dama hakan kan haifara da rade-radin mutuwarsa.