Isra'ila ta kama Falasdinawa tara bayan yahudawa sun ƙulle su a gidajensu
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na Wafa ya ce dakarun Isra'ila sun kama Falasdinawa tara na iyali guda bayan sun shafe sa'o'i suna maƙale a gidansu sakamakon wani hari da yahudawa kama wuri zauna suka kai.
Rahoton ya ce maharan sun kewaye gidan Mohammad Sabet Majid Hassoun da ke wajen ƙauyen Beit Imrin, arewa maso yammacin Nablus, na fiye da sa'o'i uku a daren Lahadi.
Daga bisani ne sojojin Isra'ila suka mamaye yankin tare da kama duka mutane tara da ke cikin gidan.
Wannan na zuwa ne yayin da wasu iyalai Falasdinawa uku ke ci gaba da kasancewa cikin gidajensu a ƙauyen Qusra da ke kudancin Nablus, bayan da yahudawan suka yi musu ƙawanya.