An tashi, West Ham 3-0 Leeds
Damar da ke gaban West Ham na hannun Everton kuma Tottenham na iya ƙoƙarinta na tsira da kwallonta ɗaya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku wainar da ake toyawa a ranar ƙarshe ta gasar Premier Ingila
Muhammad Buhari Fagge
Damar da ke gaban West Ham na hannun Everton kuma Tottenham na iya ƙoƙarinta na tsira da kwallonta ɗaya.
Callum Wilson (90+4 mins)⚽️
Ko kwallayen za su yi wa West Ham amfani,
Yanzu suna jira su ji sakamakon wasan Tottenham domin sanin makomarsu.
An kara minti 10 a wasan.
Burin Brentford na Europa na dab da cika.
A cire Mo Salah, wasansa na ƙarshe a ƙungiyar Liverpool.
An shiga rudani a filin wasa na Anfield, magoya baya na ta zubar da hawaye.
Jean-Philippe Mateta (89 mins)⚽️
Phil Foden (90+1 mins)⚽️
Amma ana dubawa.
VAR ta kashe kwallon
Fulham ta yi canji:
Shiga - Josh King, Harry Wilson, Tom Cairney, Raul JImenez.
Fita - Kevin, Emile Smith Rowe, Oscar Bobb, Rodrigo Muniz.
Tom Cairney (81 mins) ⚽️
Jarrod Bowen ⚽️
Ko shakka babu West Ham na yunwar maki uku a wasan nan.
Villa ta yi canji uku.
Shiga: Amadou Onana, Youri Tielemans, Pau Torres.
Fita: Lamare Bogarde, Douglas Luiz, Victor Lindelof.
Tuni labari ya ishi Tottenham da magoya bayanta kan farkewar da West Ham ta yi.
A ko wanne wasa matsin lamba na ƙaruwa.
Taty Castellanos (67 mins)⚽️
A halin da ake ciki West Ham na da kwarin gwiwa.
A ƙarshe dai West Ham ta samu ta ci kwallo ɗaya a bugun kwanar da Jarrod Bowen ya yi shi kuma Taty Castellanos ya jefa ta.
Kallo ya koma kan Everton.........
An kori Wesley Fofana bayan katin gargaɗi na biyu da aka ba shi.
Ya taka ɗan wasan Sunderlamd ne Wilson Isidor abin da ya sa aka kore shi kenan.
Kevin Schade (64 mins)⚽️
An mayar da hannun agogo baya.
Wato kusan duk kwallo a wasannin da ake bugawa tana da tasiri, tana sauya teburi kuma.
Ollie Watkins (63 mins)⚽️
Wannan nasara za ta rikita abubuwa a damar da ƙungiyoyin Premier ke da ita na zuwa Champions Lig su shiga.
Sauyi uku daga Brighton da ke karɓar baƙuncin wasa. Carlos Baleba, Solly March da kuma Charalampos Kostoulas suka maye gurbin James Milner, Diego Gomez da Danny Welbeck.
A gefe guda kuma United ta cire Dorgu ta maye gurbinsa da matashin ɗan wasa Shea Lacey.
Muna ganin ruwan kwallaye tun da aka dawo hutun rabin lokaci.
Ko kwallo nawa za a ci gabanin a ƙare wasannin, a ranar ƙarshe ta Premier.
Curtis Jones (58 mins)⚽️ wannan labari zai yi wa Brighton daɗi ita da ke neman gurbin Europa
Zian Flemming⚽️
Cole Palmer (56 mins)⚽️