Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 13/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 13/08/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. ADC ta zargi hukumomi da yunƙurin kama Aregbesola

    Jam'iyyar ADC mai hamayya a Najeriya ta zargi hukumomin tsaron ƙasar da kitsa kama sakatarenta na ƙasa, Rauf Aregbesola gabanin zaɓen gwamnan jiharsa ta Osun da ke tafe.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta ce ta samu ''sahihan bayanan sirri'' na shirin kama sakataren jam'iyyar na ƙasa, wanda kuma shi ne tsohon gwamnan jihar Osun.

    Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta, ko wata hukumar tsaro a ƙasar da ta tabbatar da wannan zargi.

    Sai dai jam'iyyar ta bayyana cewa zargin shirin na da matuƙar tayar da hankali, musamman idan aka yi la’akari da abin da ta kira ci gaba da tsoratarwa da muzgunawa da kuma amfani da cibiyoyin gwamnati ta hanyoyin da ba su dace ba don muzguna wa ƴan hamayya.

    Aregbesola ya kasance gwamnan Jihar Osun daga shekarar 2010 zuwa 2018, sannan daga ya zama ministan cikin gida zamanin gwamnatin Buhari.

  2. Gwamnatin Sokoto za ta raba wa jami’an tsaro babura 1,000 domin inganta tsaro

    Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe Naira biliyan 1,759,250,000 domin sayen babura ƙirar Bajaj guda 1,000 da za a raba wa hukumomin tsaro a jihar, domin ƙarfafa yaƙi da ƴanbindiga.

    A cewar daraktan janar na yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, an amince da wannan buƙatar ne a majalisar zartarwar jihar.

    Bawa ya ce, “Sayen babura guda 1,000 na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin ƙara wa jami’an tsaro kayan aiki da za su taimaka wajen gudanar da ayyukansu a wuraren da matsalar ƴanbindiga ta fi ƙamari.”

    Ya ƙara da cewa sayen baburan zai kasance ƙarin tallafi ne ga motocin yaƙi masu sulke guda 62 da gwamnatin jihar ta saya kwanan nan, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 27.

    A cewar Bawa, “Gwamnatin jihar ta riga ta samar da motocin sulke guda 62 da aka raba wa hukumomin tsaro, kuma wannan sabon shirin na sayen babura zai ƙara ƙarfafa ayyukan sintiri da sauran ayyukan tabbatar da tsaro.”

    Baya ga batun tsaro, Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da wasu ayyuka da dama da suka shafi ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da bunƙasa sana'o'i.

    Daga cikin ayyukan akwai ware Naira miliyan 723,171,671.23 domin gyara makarantar Government Technical College da ke Runjin Sambo, yayin da aka amince da kashe Naira miliyan 498,995,000 domin gyaran A.A. Raji Special School.

    Haka kuma, an ware Naira miliyan 489,319,380 domin gyaran kashi na farko na College of Nursing Sciences, sannan Naira miliyan 229,363,455 domin gyaran dakunan kwanan dalibai maza da mata na College of Basic and Remedial Studies.

    A fannin noma, an amince da Naira miliyan 174,642,000 domin gyaran gidajen ma'aikata da inganta katangar College of Agriculture and Animal Science da ke Wurno.

    Majalisar ta kuma amince da Naira miliyan 133,665,861.32 domin gina katangar Wamakko Primary Health Centre.

    A kokarin ƙarfafa sana'o'in mata, gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 93,880,000 domin sayen kayan koyon sana'a ga cibiyoyin koyon sana'a na mata guda 46 da ke faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

  3. 'Mayaƙan Houthi da na al-Shabab na yunƙurin ƙwace Mashigar Bab al-Mandab'

    Jaridar The Telegraph ta Birtaniya ta wallafa wani rahoto mai taken: "Mayaƙan Houthi na shirin buɗe sabon babi a yaƙin Iran, bayan yunƙurin rufe wata muhimmiyar mashigar ruwa ta biyu."

    Jaridar ta ce mayaƙan Houthi, waɗanda a yanzu ake kallonsu a matsayin mafiya ƙarfi cikin ƙungiyoyi masu alaƙa da Iran a yankin, suna shirye-shiryen rufe mashigar Bab al-Mandab domin amfanin Iran, da nufin ƙara matsin lamba kan shugaban Amurka Donald Trump, lamarin da zai iya ƙara jefa tattalin arzikin duniya cikin matsala.

    Rahoton ya ce akwai haɗin gwiwa tsakanin mayaƙan na Houthi da ƙungiyar al-Shabaab da ke Somalia, wanda manufarsu ita ce mallake ɓangarori biyu na mashigar Bab al-Mandab tare da rufe ta idan Iran ta yanke shawarar yin hakan.

    Rahoton ya ambato wata majiya da ta ce mayaƙan Houthi na miƙa fasahar ƙera da amfani da jiragen sama marasa matuƙa (drones) na Iran ga ƙungiyar al-Shabaab bisa umarnin Tehran.

    Manufar hakan, in ji rahoton, ita ce haifar da yanayi a Bab al-Mandab mai kama da wanda ake gani a mashigar Hormuz.

    Jaridar ta ce kimanin kashi 10 zuwa 12 cikin 100 na cinikayyar duniya na bi ta mashigar Bab al-Mandab, wadda ke haɗuwa da Mashigar Suez.

    Telegraph ta yi gargaɗin cewa idan aka rufe mashigar, jiragen ruwa za su tilasta bin wata hanya ta daban wadda za ta ƙara musu makonni suna zagayawa ta kudancin Afirka, lamarin da zai ƙara kuɗaɗen sufuri.

  4. Al'ummar Zambiya na zaɓen sabon shugaban ƙasa

    Al'ummar Zambiya na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin ƙasar.

    Ana kallon zaɓen a matsayin ma'aunin gwajin ingancin dimokuraɗiyya a ƙasar mai tarihin 'ɗorewar tsarin dimokuraɗiyya a Afrika.

    Shugaban ƙasar Hakainde Hichilemana wanda ke neman wa'adi na biyu na da farin jini sakamakon rawar da ya taka lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki.

    Akwai damuwa game da ƙaruwar rashin aikin yi.

    Ana ganin za a fafata ne tsakanin shugaban ƙasar da jagoran adawa Brian Mundibile wanda magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu ke mara wa baya.

    Ɗan takarar shugaban ƙasa dai na buƙatar sama da kashi 50 na ƙuri'u kafin ya yi nasara.

  5. Amurka ta soki Isra'ila kan ci gaba da zaman sojojinta a Lebanon

    Amurka ta yi Allah wadai da ƙawarta Isra'ila, a wani yanayi da ba kasafai ake ganin irinsa ba, bayan ministan tsaron Isra'ila ya dage sojojinsa za su ci gaba da zama a kudancin Lebanon.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana sa rai Isra'ila za ta yi amfani da tsarin yarjejeniyar janye sojoji.

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ne ya yi waɗannan kalamai yayin da ya ziyarci kudancin Lebanon, inda ya tabbatar da yadda sojojinsa ke rusa dukkan gidajen yankin.

    Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya ce ɓarnar da Isra'ila ke yi ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

    Yarjejeniyar ta ƙunshi janye dakarun Isra'ila daga yankunan yayin da sojin Lebanon za su ƙwace makaman ƴan Hezbollah.

    Ministocin Isra'ila na ƙara zafafan kalaman ne a lokacin da zaɓe ke ƙaratowa.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Ahamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.