Fitacciyar mawaƙiya, jaruma kuma marubuciyar waƙoƙi ta Amurka, Dolly Parton, ta rasu tana da shekara 80 a duniya.
An haifi Dolly Rebecca Parton a ranar 19 ga Janairun 1946 a jihar Tennessee ta Amurka, inda ta taso cikin iyali mai yara 12.
Tun tana ƙarama ta fara rubuta waƙoƙi kuma ta shiga harkar kiɗa, lamarin da ya sa daga baya ta zama ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan waƙoƙin country a tarihin Amurka.
Dolly Parton ta yi fice da waƙoƙi irin su Jolene, I Will Always Love You da kuma 9 to 5, waɗanda suka samu karɓuwa a faɗin duniya.
Baya ga harkar waƙa, ta yi fice a fina-finai da dama, sannan ta kafa cibiyar nishaɗi ta Dollywood da kuma shirin Imagination Library, wanda ke raba littattafai kyauta ga yara domin ƙarfafa karatu.
A tsawon aikinta, ta lashe lambobin yabo da dama ciki har da Grammy, kuma ta sayar da sama da kwafi miliyan 100 na ƙundin waƙoƙinta.
Mutuwar Dolly Parton ta jawo alhini daga magoya bayanta da masu sha'awar kiɗa a duniya, inda ake yi mata kallon ɗaya daga cikin fitattun mata da suka canza fagen waƙoƙin country.
Ba saboda nasarorin da ta samu a harkar nishaɗi kaɗai aka santa ba, har ma saboda ayyukan jin ƙai da tallafin da ta riƙa bayarwa ga yara da al'ummomi masu buƙata.