Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 11/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Asabar 11/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Su wane ne wakilan Amurka da Iran a tattaunawar Pakistan?

  2. Muna kiran Amurka da Iran su shiga tattaunawar da zuciya ɗaya - MDD

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi maraba da tattaunawar zaman lafiya da Amurka da Iran suka amince za su yi, inda ya buƙaci ɓangarorin biyu su shiga tattaunawa da ''zuciya ɗaya''.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai, kakakin Gutteres, Stephane Dujarric ya ce babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya yi kira ga duka ɓangarorin biyu su yi amfani da damar tattaunawar wajen kawo ƙarshen rikicin ta hanyar amincewa da cikakkiyar yarjejeniyar.

    "Babban sakataren ya jaddada cewa babu wata hanyar kawo ƙarshen yaƙin cikin zaman lafiya da ta wuce hanyar diplomasiyya,'' in ji Dujarric.

    Jakadan Guterres na musamman ya isa yankin domin tallafa wa yunƙurin diplomasiyyar.

  3. Muna fatan samun tattaunawa mai amfani - Pakistan

    Ministan harkokin wajen Pakistan, Mohammad Ishaq Dar ya yaba wa Amurka kan burinta na samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.

    Mista Dar ya bayyana hakan ne lokacin da yake tarbar tawagar Amurka ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, JD Vance lokacin da suka isa Islamabad domin tattaunawa da wakilan Iran bisa shiga tsakanin Pakistan domin kawo ƙarshen yaƙin Iran da AMurka da kuam Isra'ila.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta fitar, ta ambato Dar na cewa yana fatan samun tattaunawa mai amfani tsakanin Iran da Amurka.

    Ya kuma jaddada burin Pakistan na ci gaba da shiga tsakanin ɓangarorin biyu har zuwa lokacin da za su cimma yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin.

  4. Ƴan sama-jannatin Amurka da suka je duniyar wata sun sauko

    Ƴan sama-jannatin nan huɗu, na kumbon Artemis II sun dawo wannan duniya tamu lami lafiya, bayan wata doguwar tafiya zuwa duniyar wata, inda suka zagaye shi kafin dawowa gida.

    A yanzu sun zamo rukunin bil'adama na farko da aka samu harbawa duniyar watan a sama da rabin ƙarni.

    Kumbon da suke ciki ya sauko da taimkon lemmomi a cikin Tekun Pasifik kusa da kudancin California bayan shafe kwanaki 10 a sararin samaniya.

    Daga nan ne aka ɗauke su zuwa wani jirgin ruwan sojin Amurka domin duba lafiyarsu.

    Hukumar kula da sararin samaniyar ƙasar NASA, ta ce suna cikin ƙoshin lafiya, tare da bayyana wannan aiki a matsayin gagarumin ci gaba a binciken sararin samaniya da ɗan Adam ke yi.

    Masana sun bayyana nasarar a matsayin muhimmin mataki a ƙoƙarin ci gaba da tura mutane duniyar watan.

  5. Wakilan Lebanon da Isra'ila za su gana da a Amurka

    Wakilai daga Lebanon da Isra’ila za su gana a birnin Washington a ranar Talata, ƙarƙashin shiga tsakanin Amurka, wata guda bayan sake ɓarkewar rikici mai muni tsakanin Isra’ila da Hezbollah.

    Ɓangaren Isra’ila ya ce a shirye yake ya tattauna abin da ya kira shawarwarin zaman lafiya da gwamnatin Lebanon.

    Sai dai ya ce ba zai tattauna yiwuwar tsagaita wuta da ƙungiyar Hezbollah ba, tare da cewa zai nemi a kwance ɗamarar ƙungiyar.

    Isra’ila na cewa hare-haren da take kaiwa a ƴan makonnin nan na shafar wuraren da Hezbollah ke da ƙarfi ne kawai, to sai dai hare-haren sama da ta kai sun kashe kusan mutane 2,000, ciki har da yara da mata da dama, da kuma likitoci da ƴan jarida da malamai.

    Asibitoci sun cika maƙil sakamakon yawan waɗanda suka jikkata.

    Fiye da mutum miliyan guda ne hare-haren suka raba da matsugunansu.

  6. Wakilan Iran sun isa Pakistan domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin ƙasar

    Wata tawaga daga Iran ta isa birnin Islamabad na Pakistan domin tattaunawa da Amurka da nufin kawo ƙarshen rikicin da aka shafe sama da makonni shida ana gwabzawa.

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, wanda ke jagorantar tawagar, ya ce a shirye Tehran take ta ƙulla yarjejeniya idan Amurka ta amince da haƙƙoƙinta.

    A baya ya ce ba za a yi wata tattaunawa ba har sai an tsagaita wuta a Lebanon.

    Idan har tattaunawar ta gudana, to kuwa zai kasance an kafa tarihi, domin za ta zamo tattaunawa mafi girma tsakanin ƙasashen biyu tun bayan juyin juya halin Musulunci na 1979.

    A gefe guda, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi wa mataimakinsa, J. D. Vance, fatan alheri yayin da zai halarci tattaunawar.

    Ya kuma ce za a buɗe mashigar Hormuz “ko da Iran ta amince ko ba ta amince ba.”

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello ke fatan sake kasancewa da ku domin kawo muku irin wainar da ake toyawa game da tattaunar kawo ƙarshen yaƙin Iran da sauran batutuwa.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.