Sojojin Najeriya sun kama ƴan ƙasashen wajen 46 a wani aikin samar da tsaro
Sojojin Najeriya sun sanar da kama ƴan ƙasashen waje 46 a wani aikin samar da tsaro da suka gudanar a jihar Ogun da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar.
A cewar rundunar, an kai samamen ne a ranar Alhamis a yankunan Ijebu Imushin da Ijebu Ilese tare da wasu ƙauyuka da ke kusa, bayan samun bayanan sirri masu muhimmanci.
Mai magana da yawun rundunar, Idereghi Samuel Akari, ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen sun shafe kusan watanni shida a Najeriya ba tare da takardun izinin zama ba.
Ya ƙara da cewa mutanen sun shaida wa jami’an bincike cewa su ‘yan kasuwa ne da ma’aikata masu alaƙa da kamfanin QNET, wani kamfanin sayar da kayayyaki ta intanet mai hedikwata a Hong Kong.
Sai dai kamfanin QNET ya sha fuskantar zarge-zarge a Najeriya, inda hukumomi ke danganta kamfanin da damfara da safarar mutane da kuma shigo da mutane ba bisa ƙa’ida ba amma kuma kamfanin ya musanta hannu a irin waɗannan ayyuka, yana mai cewa yana nesanta kansa da masu amfani da sunansa wajen aikata laifi.
Kamen na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa a yammacin Afirka kan wasu ƙungiyoyin da ake zargi da amfani da sunan kamfanin wajen yaudarar mutane da alƙawuran samun aiki a ƙasashen waje da kuma samun kuɗi cikin sauƙi.
Daga cikin mutanen da aka kama, guda 18 ‘yan ƙasar Burkina Faso ne, 23 kuma daga Ivory Coast, huɗu daga Togo yayin da kuma mutum ɗaya daga Senegal ne.
Daga bisani, an miƙa waɗanda aka kama ga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya domin ci gaba da bincike.