Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Argentina za ta buga wasan karshe da Sifaniya a gasar kofin duniya

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen kusa da karshe
Ingila 1 , Argentina 2 a cikakken lokaci
Ingila
Argentina
Full time
Hutun rabin lokaci Ingila 0 , Argentina 0

Muhimman abubuwa

Ingila

  • A. GordonGoal 55 minutes

Argentina

  • E. FernándezGoal 85 minutes
  • Lautaro MartínezGoal 90 minutes plus 2
Ba da ƙwallo a ci
Ingila,M. Rogers (55 minutes)
Argentina,L. Messi (85 minutes, 90 minutes plus 2)

Taƙaitattu

  • Ingila da Argentina za su kara a wasan daf da karshe a gasar cin kofin duniya
  • Duk wadda ta yi nasara za ta haɗu da Sifaniya a wasan karshe ranar Lahadi
  • Za a buga wasan neman mataki na uku da Faransa da duk wadda aka ci tsakanin Ingila da Argentina ranar Asabar
  • Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
  • Sifaniya ta doke Faransa ta kai zagayen karshe a ranar Talata a gasar kofin duniya

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. An tashi wasan, Ingila 1-2 Argentina

    Mafarkin Ingila na lashe kofin duniya ya zo karshe, za ta buga neman mataki na uku da Faransa ranar Asabar.

    Argentina mai rike da kofin za ta kara da Sifaniya ranar Lahadi.

  2. , Ingila 1-2 Argentina

    Ya kwan da sanin sai dai ya buga neman mataki na uku a gasar cin kofin duniya ranar Asabar.

  3. , Ingila 1-2 Argentina

    Bellingham ya yi wa Messi keta ya fadi kasa, nan da nan yan wasan Argentina suka yi kanshi, amma alkalin wasa na kokarin kwantar da hankalin yan wasa.

  4. , Ingila 1-2 Argentina

    An cire rigunan ana jujjuya su daga magoya bayan Argentina.

  5. GOAL -England 1-2 Argentina, Lautaro Martinez

    Kwallo ce Messi ya bugo daga gefe, nan da nan Martinez ya yi tsalle ya sa kai ta fada raga.

    Kuma daf ake a tashi daga wasan.

  6. GOAL - England 1-1 Argentina, Enzo Fernandez

    Kwallo ce mai kyau da Enzo Fernandez ya ci daga yadi na 20 ta fada ragar Ingila.

    Wasa ya koma danye.

  7. , Ingila 1-0 Argentina

    Lionel Messi ya yi ƙoƙari ya lanƙwasa kwallon zuwa cikin rage, amma Jordan Pickford yana kallon shi a baya.

  8. , Ingila 1-0 Argentina

    Ingila tana da minti 10 da karin lokaci nan gaba zuwa wasan karshe a gasar cin kofin duniya a karon farko a cikin shekaru 60.

  9. , Ingila 1-0 Argentina

    Ingila ta rike wasan nan Argentina ta rasa yadda za ta farke kwallon da aka zura mata a raga

    Lionel Messi da Nico Gonzalez suna shawarar yadda za su fasa bayan Ingila.

  10. , Ingila 1-0 Argentina

  11. Kwallo ta bugi turke, Ingila 1-0 Argentina

    Kdan ya rage Alexis Mac Allister ya ci kwallo.

  12. Ingila ta yi canjin dan wasa, Ingila 1-0 Argentina

    Ezri Konsa ya maye gurbin dan wasan Anthony Gordon.

  13. An je hutun shan ruwa, Ingila 1-0 Argentina

    Yau she muka koma zagaye na biyu, amma har an je hutun shan ruwa.

    Yanzu wasa yana zafi fiye da zangon farko, tunda Ingila ta ci kwallo, Argentina na son farkewa.

  14. , Ingila 1-0 Argentina

    Argentina ta danna da yawa tana son farke kwallon, kuma kadan ya rage Messi ya farke, amma Fickford ya sa hannu ya tura ta waje.

  15. , Ingila 1-0 Argentina

    Kwallon mai kyau daga Lionel Messi zuwa da Nico Gonzalez, wanda ya yi kokarin saka kai, amma John Stones da yake yana da tsayi ya riga shi.

  16. Argentina ta yi canji, Ingila 1-0 Argentina

    Nico Gonzalez ya maye gurbin Leandro Paredes. Kai tsaye aka yi wannan canjin.

  17. Spence ya ceci Ingila, Ingila 1-0 Argentina

  18. , Ingila 1-0 Argentina

    Argentina ta samu dama mai kyau, sai dai Spence ya bata kwallon da ta kai Argentina na korafin fenariti, amma an bayar da bugun kusurwa.

    Argentina ta buga amma Ingila ta fitar da kwallon ba wani hadari.

  19. GOAL - England 1-0 Argentina, Anthony Gordon

    Kwallo ce mai kyau ya ci Argentina, bayan da aka sharo kwallon daga kusurwa, sai Godon ya shiga gidan Argentina ya kuma taba ta fada raga.

  20. , Ingila 0-0 Argentina

    Argentina na kai kora, amma ba ta samu wata damar cin kwallo ba, Ingila na kokarin cire kwalon kada ta zamar mata hadari.