Mbappe da Dambele za su wakilci Faransa a gasar kofin duniya 2026, Gasar kofin duniya
Kylian Mbappe da mai riƙe da ƙyautar Ballon d'Or, Ousmane Dembele, suna cikin jerin ƴan wasa 26 da za su wakilci Faransa a gasar cin kofin duniya a 2026.
Olivier Giroud ne kan gaba a yawan ci wa tawagar ƙwallaye fiye da Mbappe, inda yake da 57 a raga, shi kuwa ɗan ƙwallon Real Madrid yana da 56.
Ana sa ran Mbappe ne zai ci gaba da ƙyaftin ɗin tawagar, wanda ke jinya da bai samu damar buga El Clasico ba da Barcelona ta yi nasarar cin Real Madrid 2-0 ta lashe La Liga kuma na biyu a jere.
Dembele kuwa ya ci ƙwallo 35 tda lashe Champions League tare da Paris Saint-Germain a kakar da ta gabata, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan Faransa na biyu a wannan ƙarni da ya lashe Ballon d'Or. Duk da haka, har yanzu bai ci ƙwallo ba a gasar kofin duniya duk da kasancewa cikin tawagar gasar biyu da suka gabata.
Michael Olise na Bayern Munich da kuma abokin wasan Dembele a PSG, Desire Doue, suna cikan jerin ƴan wasan a gurbin masu cin ƙwallaye, yayin da ɗan wasan Manchester City Rayan Cherki da kuma mai tsaron bayan Arsenal, William Saliba ke cikin ƴan wasa bakwai daga Premier League.
Lucas Hernandez da ɗan wasan tsakiya N'Golo Kante da Mbappe da Dembele suna cikin ragowar tawagar Faransa da ta lashe kofin duniya a 2018.
Deschamps, wanda ya kai Faransa wasan ƙarshe a kofin duniya sau biyu a jere, ya gayyaci wasu ƴan wasa da aka yi mamaki, wanda daga wannan gasar zai yi ritaya a matsayin kocin Faransa.
Ba a saka ɗan wasan Real Madrid Eduardo Camavinga da na Tottenham, Randal Kolo Muani cikin waɗanda aka sanar ba, duk da cewa suna cikin tawagar 2022.
Haka kuma mai tsaron ragar PSG, Lucas Chevalier bai samu gurbi ba, inda mai tsaron ragar Lens, Robin Risser wanda bai taɓa bugawa Faransa wasa ba tare da Brice Samba suna matsayin masu taimaka wa Mike Maignan.
Hugo Ekitike na Liverpool, wanda ya samu mummunan raunin a watan Afrilu na jinya, har karshen kakar bana, ba zai buga gasar kofin duniya ba.
Faransa za ta fara wasanninta da Senegal a New Jersey ranar 16 ga watan Yuni, sannan ta kara da Iraq ranar 22 ga watan Yuni da kuma Norway ranar 26 ga watan Yuni a rukuni na I.
Tawagar ƴan wasan Faransa da za su buga kofin duniya a 2026
Masu tsaron raga: Mike Maignan (AC Milan), Robin Risser (Lens), Brice Samba (Rennes)
Masu tsaron baya: Lucas Digne (Aston Villa), Malo Gusto (Chelsea), Lucas Hernandez (Paris St-Germain), Theo Hernandez (Al Hilal), Ibrahima Konate (Liverpool), Maxence Lacroix (Crystal Palace), Jules Kounde (Barcelona), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamenaco (Bayern Munich)
Masu buga tsakiya: N'Golo Kante (Fenerbache), Manu Kone (Roma), Adrien Rabiot (AC Milan), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Warren Zaire-Emery (Paris St-Germain)
Masu cin ƙwallaye: Maghnes Akliouche (Monaco), Bradley Barcola (Paris St-Germain), Rayan Cherki (Man City), Ousmane Dembele (Paris St-Germain), Desire Doue (Paris St-Germain), Michael Olise (Bayern Munich), Kylian Mbappe (Real Madrid), Jean-Phillipe Mateta (Crystal Palace), Marcus Thuram (Inter Milan)