Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwaftan ƙasashe da kuma sauran sassan duniya na ranar Asabar 21 ga watan Agustan 2026.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. IRNA: Iran ta ba wasu jiragen Iraqi izinin wucewa ta mashigar Hormuz

    Kamfanin dillancin labarai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, IRNA, ya wallafa wani rahoto na musamman cewa Iran ta ba da izini ga wasu tankokin dakon man Iraqi “su ratsa mashigar Hormuz”, bayan da Iraqi ta yi ta neman hakan sau da dama.

    Rahoton ya bayyana cewa an aika buƙatun izinin wucewar tankokin Iraqi zuwa Iran “sau da yawa ta hanyoyi daban-daban.”

    IRNA ta kuma ce a lokacin ziyarar Mohammad Baqer Qalibaf zuwa Iraqi, “ba da izini na musamman” ga tankokin dakon man da ke mallakar ƙasar domin su ratsa mashigar Hormuz shi ne “buƙata mafi muhimmanci” da hukumomin Baghdad suka gabatar.

    Harkokin zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen safarar mai da iskar gas a yankin, sun ragu matuƙar gaske.

  2. Su wane ne za su jagoranci yaƙin neman sake zaɓenTinubu?

    A daidai lokacin da da 'yan Najeriya ke fara lissafe-lissafen yadda yakin zaben badi zai kasance, shugaban kasar Bola Tinubu ya fitar da kwamitin yakin neman sake zabensa a babban zaben kasar na shekarar 2027.

    A makon da ya gataba ne dai a hukumance aka fara yakin neman zabe, kamar yadda jadawalin zaben kasar, wanda hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato INEC ta tsara.

    A cikin jerin sunayen da aka fitar a safiyar Asabar, an naɗa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta Janar (DG) na kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC.

    Karanta cikakken labarin a nan.

  3. TikTok za ta biya tarar dala miliyan 400 saboda keta haƙƙin sirrin yara

    TikTok ta amince da biyan dala miliyan 400 domin sasanta wata ƙara da aka zarge ta da keta haƙƙin sirrin yara, a ɗaya daga cikin manyan yarjejeniyoyin sasanta shari’a da aka taɓa samu a tarihi.

    Yarjejeniyar ta biyo bayan wata ƙara da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta shigar a shekarar 2024, a lokacin mulkin tsohon Shugaban Amurka Joe Biden.

    Ƙarar ta yi zargin cewa TikTok da asalin kamfaninsa mai suna ByteDance, sun tattara “ɗimbin bayanai” kan miliyoyin masu amfani da manhajar waɗanda shekarunsu bai kai 13 ba.

    An ce wannan mataki ya saɓa wa dokar tarayya ta Children’s Online Privacy Protection Act (COPPA), wadda aka yi a shekarar 2000. Wanda ita ce dokar da wasu jihohin Amurka da dama suka kuma shigar da ƙara kan Meta bisa zargin yi mata karan-tsaye.

    “Yara da iyaye sun fi samun kariya a yau fiye da lokacin da aka fara wannan shari’ar,” in ji Mataimakin Babban Lauyan Amurka Brett Schumit.

    Sauran kamfanonin da suka biya tarar kuɗi ga gwamnatin Amurka saboda keta wannan doka sun haɗa da YouTube, wanda ya biya dala miliyan 170 a shekarar 2019, da Epic Games, wanda aka ci tararsa da dala miliyan 275 a shekarar 2022.

    Meta, kamfanin da ya mallaki Instagram da Facebook, shi ma na iya fuskantar manyan tarar kuɗi saboda zargin keta dokar. Manyan lauyoyin jihohi a jihohin Amurka 29 ne suka shigar da ƙarar. Tarar na iya haura daruruwan biliyoyin daloli.

    An fara sauraron shari’ar Meta a wannan makon, inda ake zargin kamfanin mai Instagram da Facebook da yunkurin jawo hankalin yara masu amfani da manhajojinsa tare da samun riba daga hakan.

  4. Tinubu ya taya ‘yar Gombe murnar lasha gasar musabaka ta duniya

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Maryam Ibrahim Dan’Azumi, ‘yar asalin Jihar Gombe murnar lashe gasar musabakar Alqur'ani bangaren mata ta duniya ta King Abdulaziz International Qur’anic Competition da aka gudanar a kasar Saudiyya.

    Maryam ta zama ta farko a rukunin mata a gasar da aka gudanar a birnin Makkah, inda ta doke sauran mahalarta daga ƙasashe 132 na duniya.

    Maryam ta samu riyalan Saudiyya 300,000, wanda ya yi daidai da kusan naira miliyan 120 a matsayin kyauta.

    Shugaba Tinubu ya yaba wa Maryam bisa ƙwarewa da bajintar da ta nuna wajen haddacewa, karatu da fahimtar Alƙur’ani mai girma. Ya ce nasarar ba ta Maryam kaɗai ba ce, inda ya ce ta zama abin alfahari ga Najeriya baki ɗaya, domin ta ɗaga darajar ƙasar a fagen duniya.

    Tinubu ya kuma bayyana Maryam da ‘yar’uwarta, Hajara Ibrahim Dan'Azumi, a matsayin abin koyi ga matasan Najeriya.

    Hajara ita ma ta samu nasara a wata makamanciyar gasar Alƙur’ani da aka gudanar a Jordan a shekarar 2024, inda ta zo ta farko.

    Shugaban Ƙasar ya yaba wa iyayensu, malamansu da masu kula da tarbiyyarsu, yana mai cewa irin wannan matsayi na ƙwarewa yana buƙatar sadaukarwa, jajircewa da kyakkyawar tarbiyya.

    A ƙarshe, Tinubu ya yi wa Maryam addu’ar Allah Ya ƙara mata ilimi da hikima, Ya kuma ba ta damar ci gaba da samun nasara a karatun Alƙur’ani da sauran abubuwan da za ta gudanar a rayuwarta.

  5. An yi amfani da mutum-mutum wajen tiyata a Najeriya

    Jihar Imo ta samu gagarumar nasara a fannin kiwon lafiya, bayan kammala tiyatar da aka yi da taimakon na’urar mutum-mutumi a karon farko a asibitin Specialist Hospital da ke Umuguma, Owerri.

    Tawagar ƙwararrun likitoci ‘yan Najeriya da na ƙasashen waje ce ta gudanar da tiyatar, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Kingsley Ekwueme, wani ƙwararren likitan tiyatar mutum-mutumi da ke aiki a Birtaniya, amma ɗan asalin Jihar Imo.

    Da yake magana da manema labarai a cibiyar Imo Robotics and Oncology Centre (IROC), inda aka gudanar da tiyatar, Farfesa Ekwueme ya bayyana aikin da “cikakkiyar nasara," kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ya jaddada cewa wannan fasaha na da matuƙar amfani wajen maganin ciwon daji na kasan mafitsara, domin a cewarsa tana bai wa likitoci damar cire ƙwayoyin da ke ɗauke da ciwon daji tare da kare muhimman ayyukan jiki, ciki har da ikon yin fitsari da karfin jima’i.

    Ekwueme ya ce nasarar tiyatar mutum-mutumi wajen maganin ciwon daji, musamman na kasan mafitsara, tana da matuƙar girma, kuma marasa lafiya bai kamata su sha fama da rashin iya riƙe fitsari ko rasa karfin jima’i na dogon lokaci bayan tiyatar ba.

    Gwamna Hope Uzodimma, wanda ya shaida wannan gagarumar nasara, ya ce hakan babban mataki ne wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya mai araha ga al’ummar jihar.

    Ya ce cibiyar ba za ta kasance wurin kula da marasa lafiya kawai ba, har ma za ta taimaka wajen gano cututtuka tun da wuri da kuma rigakafinsu ta hanyar duba lafiyar jama’a akai-akai.

    Uzodimma ya bayyana cewa cibiyar tana aiki ne ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP), inda mafi yawan kuɗaɗen gudanar da ita ke fitowa daga ɓangaren masu zaman kansu. A cewarsa, hakan zai taimaka wajen tabbatar da dorewar cibiyar da ingantaccen gudanar da ita.won lafiya na musamman.

  6. ICPC ta sake bankado wata hukumar bogi a Najeriya

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wata sabuwar hukumar gwamnati da ake zargin ta bogi ce, wadda hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasar ta gano.

    Wannan lamari ya biyo bayan wani makamancin bincike da ya shafi wata hukuma da gwamnati ta ce an gabatar da ita a matsayin hukumar gwamnati, alhali ba haka ba ne.

    Hukumar ICPC ta ce hukumar ta National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office tana gudanar da ayyukanta ba bisa ƙa’ida ba daga wani ofishin gwamnati da ke Abuja.

    Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, ya ce an ware wa hukumar wannan ofishin ne a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ba tare da amincewar Shugaban Ƙasa ba.

    Ya bayyana cewa an gano hakan ne yayin wani babban bincike da Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a gudanar, bayan wani rahoto na baya da ya shafi Presidential Foreign Intervention Promotion Council, wadda ake zargin ƙungiya ce da ba ta wanzu a zahiri.

    A cewar Aliyu, wani mutum mai suna George Buchi Nwabueze ne ya ke tallata sabuwar hukumar, kuma ana zargin yana amfani da sunaye daban-daban.

    ICPC ta ce tana binciken yadda aka ba wannan ofishi damar gudanar da ayyukansa daga harabar gwamnati, da kuma ko wasu jami’an gwamnati sun taimaka wajen ba shi damar yin hakan.

    Har yanzu ba a bayyana ko Nwabueze ya samu kuɗi daga wannan zargin ba kafin a gano lamarin.

    A cewar ICPC, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a kama Nwabueze ba tare da bata lokaci ba.

    Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin dakatar da wasu manyan jami’an gwamnati da ake zargi suna da alaka da hukumar, in ji Aliyu.

    A baya dai wani bincike daban da aka gudanar kan Presidential Foreign Intervention Promotion Council, wadda fadar shugaban ƙasa ta ce ba ta bogi ce.an hukumomin da ake zargin na bogi ne.

  7. Sakataren sojin kasan Amurka zai yi murabus

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga Mujallar Wall Street cewa ana sa ran Sakataren Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka, Dan Driscoll, zai yi murabus kafin ƙarshen shekara, bayan watanni ana samun takun-saka tsakaninsa da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth.

    Mujallar Wall Street Journal ta wallafa rahoton ne bisa bayanan wasu mutane da ke da masaniya kan dambarwar.

    Sai dai Reuters ta ce har yanzu ba ta samu damar tabbatar da rahoton da kanta ba.

    Idan aka tabbatar da murabus ɗin Driscoll, hakan zai sa Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka ta kasance ba tare da shugaba da Majalisar Dattijan Amurka ta tabbatar da nadinsa ba, a daidai lokacin da Washington ke ci gaba da yaƙi da ta ƙaddamar tare da Isra’ila kan Iran, wanda yanzu ya shafe kusan wata shida.

  8. APC ta nada Abdulaziz Yari Darakta-Janar na yakin zaben Tinubu

    Jam’iyyar APC ta kafa Kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa, inda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya kasance Darakta Janar (DG) na kwamitin.

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima za su kasance shugaba da mataimakin shugaban kwamitin, sannan Gwamna Hope Uzodimma kuma zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.

    A cikin tsarin kwamitin, an haɗa manyan jami’an jam’iyyar da gwamnati domin jagorantar shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen da ake tunkarar zaɓen Janairu 2027.

    Shugaba Tinubu ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru domin ganin APC ta samu nasara a zaɓen.

  9. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar a wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.