Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a duniya 05/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwa kan Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 5 ga watan Yulin 2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Netanyahu ya san wane ne jagora a tsakaninmu - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya san wane ne jagora a tasakaninsu yana mai jaddada cewa dangantakar da ke tsakaninsu tana da ƙarfi duk da rahotannin da ke nuna akwai saɓani kan wasu batutuwa.

    Trump ya bayyana hakan ne a wata gajeriyar hira da ya yi da kafar Axios, inda ya ce: "Muna da kyakkyawar alaƙa, kuma Netanyahu ya san wane ne jagora."

    Kalaman na Trump na zuwa ne yayin da ake sa ran Netanyahu zai kai ziyara Fadar White House nan ba da jimawa ba.

    Idan ganawar ta tabbata, za ta kasance ta farko tsakanin shugabannin biyu tun bayan fara yaƙin Iran.

    Rahotanni sun nuna cewa akwai saɓanin ra'ayi tsakanin Trump da Netanyahu kan yadda ake tafiyar da wasu batutuwan tsaro, ciki har da yaƙin Iran da kuma matakan da Isra’ila ke ɗauka a Lebanon.

  2. Najeriya ta yi Allah-wadai da kashe ƴanƙasarta biyu a Afirka ta Kudu

    Najeriya ta yi Allah wadai da zargin kashe wasu 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu, tare da kira ga hukumomin ƙasar da su gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce ana zargin jami'an rundunar 'yan sandan Tshwane Metro da kashe ɗaya daga cikin mutanen a birnin Pretoria a ranar 28 ga Yuni.

    Ma'aikatar ta kuma ce wani ɗan Najeriya ya rasu bayan wasu da ba a tantance ba sun harbe shi a wajen shagon kasuwancinsa da ke garin Witbank a lardin Mpumalanga.

    Har zuwa yanzu, hukumomin Afirka ta Kudu ba su fitar da wata sanarwa kan waɗannan zarge-zarge ba.

    A wani lamari makamancin haka, an samu saɓani na diflomasiyya tsakanin Afirka ta Kudu da Ghana bayan Ghana ta ce an kashe ɗaya daga cikin 'yan ƙasarta yayin zanga-zangar adawa da baƙi a Cape Town. Sai dai hukumomin Afirka ta Kudu sun musanta wannan zargi, inda suka ce ba su da wani bayanin da ke tabbatar da irin wannan kisa.

  3. Iran da Qatar sun dawo da harkokin kasuwancin teku bayan wata biyar

    Mashawarcin harkokin kasuwancin Iran a Doha ya sanar da cewa Iran da Qatar sun sake dawo da harkokin kasuwancin teku tsakanin ƙasashen biyu bayan dakatarwar da ta ɗauki watanni biyar.

    Sanarwar ta zo ne bayan da Qatar ta bayyana cewa zirga-zirgar jiragen ruwa da sauran ayyukan ruwa a yankunanta sun koma yadda aka saba.

    A wani ɓangare kuma, yayin da Mojtaba Khamenei bai halarci sallar jana'izar mahaifinsa ba, ’ya’yan marigayin maza uku sun halarci jana’izar da aka gudanar a wani masallaci da ke birnin Tehran.

    Rahotanni sun nuna cewa ba a gayyaci tsoffin shugabannin ƙasar Iran zuwa wajen taron jana’izar ba.

  4. Rasha ta yi wa Amurka bayani game da yaƙin Ukraine

    Fadar Kremlin ta ce Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya tattauna ta wayar tarho da Shugaban Amurka Donald Trump, sa'o'i kaɗan bayan da Mista Trump ya yi irin wannan tattaunawa da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky domin bikin ranar samun ƴancin kan Amurka.

    Wani mai bai wa shugaba Putinn shawara, Yuri Ushakov, ya ce shugaban na Rasha ya yi wa takwaransa na Amurka bayani kan halin da ake ciki a fagen daga, yayin da Mista Trump ya bayyana aniyarsa ta taimakawa wajen samo mafita ga yaƙin Ukraine.

    Tun da farko, Rasha ta yi gargadin cewa zata mayar da kakkausan martani akan wani mummuna harin jirage marasa matuƙa da Ukraine ta kai cikin dare kan birnin St Petersburg da yankunan da ke kewaye da shi.

    Hukumomin Rasha sun ce za su ɗauki mataki kan harin, yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.

  5. Ana zanga-zangar buƙatar Firaministan Albania ya sauka

    Dubban masu zanga-zanga sun hallara a tsakiyar Tirana, babban birnin Albania, a rana ta 35 a jere ta abin da ake kira "juyin-juya-halin Flamingo", domin nuna adawa da wani gagarumin aikin gina wurin shaƙatawa da ake alaƙanta shi da Ivanka Trump, ƴar tsohon shugaban Amurka Donald Trump, da mijinta Jared Kushner.

    Masu zanga-zangar, sun sake bayyana buƙatarsu ta cewa Firaministan ƙasar, Edi Rama, ya yi murabus.

    A yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan aikin, wata tawagar bincike ta tarayyar turai, ta yi gargaɗin cewa tattaunawar shigar Albania cikin tarayyar turai na iya fuskantar barazana idan gwamnatin Mista Rama ta ci gaba da aiwatar da shirin gina katafaren wurin shaƙatawar na alfarma da kuɗinsa ya kai yuro biliyan biyar.

  6. Za mu cigaba a kare haƙƙin Amurkawa - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabi a birnin Washington, a yayin wani babban taro na murnar cika shekara 250 da samun ƴancin kan ƙasar daga Birtaniya.

    Jawabin, wanda ya fi karkata kan tarihin ƙasar, ya ƙunshi wasu batutuwa na siyasa, ciki har da suka ga abin da ya kira “ƴan kwaminisanci” da kuma alƙawarin ci gaba da kare haƙƙin Amurkawa na mallakar makamai.

    An jinkirta fara taron da aka shirya yi a wani babban fili taro na kasa saboda kwashe mahalarta taron da aka yi bayan fargabar da aka nuna ta fuskantar barazanar tsawa da guguwa mai karfi.

    Bukukuwan murnar cika shekara 250 da samun ƴancin kan Amurkan, sun fuskanci suka inda masu adawa da Mista Trump ke zarginsa da mayar da bikin wani dandali na siyasa.

    Wasu daga cikin ƴan jam’iyyar Democrat ma sun kaurace wa wasu daga cikin abubuwan da aka shirya domin bikin.

  7. Za mu ɗaukaka ƙara kan hukuncin hana saka hijabi a makarantar Ibadan - MURIC

    A Najeriya, ƙungiyar kare haƙƙoƙin Musulmi ta MURIC, ta yi watsi da hukuncin da wata kotun ɗaukaka ƙara da ke garin Badun na jihar Oyo, ta yanke, wanda ya soke wani hukunci da ya yarje wa ɗalibai mata su riƙa sanya hijabi a makarantar International School da ke jami'ar Ibadan.

    Kungiyar ta lashi takobin jayayya kan hukuncin har zuwa kotun koli, kuma har ta fara bin matakan da suka kamata game da hakan, domin a cewarta, ta gano hukuncin yana cike da kura-kurai.

  8. Muna cigba da ƙoƙarin ceto ɗaliban Oyo - Rundunar soji

    Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce dakarun soji na cigaba da ƙoƙarin domin ceto ɗalibai 39 da malamai bakwai da aka sace a Jihar Oyo.

    Shaibu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Asabar a Fatakwal na jihar Rivers, a cikin bukuwan ranar sojojin Najeriya ta shekarar 2026.

    An yi garkuwa da ɗalibai da malamai ne a ranar 15 ga Mayu daga makarantu uku da ke ƙaramar hukumar Orire a Jihar Oyo.

    “Yanzu haka ana ci gaba da ƙoƙari domin kuɓutar da ɗaliban, kuma muna ganin akwai alamar nasara bisa ga dukkan alamu, in ji shi kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.

    Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa za su samu nasarar ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da miƙa su ga iyalansu.

  9. Za mu ci gaba da girmama ƴancin gudanar da addini a Najeriya - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa na ba da fifiko wajen tabbatar fahimtar juna a tsakanin addinai da kuma inganta zaman lafiyar ƙasar.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Archbishop Paul R. Gallagher, sakataren hulɗa da ƙasashe da ƙungiyoyi na Vatican, wanda ya ziyarci shugaban tare da rakiyar ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Bianca Ojukwu.

    Shugaba Tinubu ya ce tattaunawa domin fahimta juna a tsakanin addinai ita ce hanya mafi dacewa wajen magance ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta.

    Ya shaida wa Archbishop ɗin cewa yana da dadaddiyar kyakkyawar alaƙa da Cocin Katolika tun lokacin da yake gwamnan Jihar Legas. Ya ce yana matuƙar alfahari da gudummawar da Cocin ke bayarwa a fannonin ilimi da kiwon lafiya.

    Tinubu ya kuma shaida wa baƙon cewa rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a baya-bayan nan, sannan ya ƙara da cewa za su ci gaba da ƙoƙari domin tabbatar da nasarar.

    A nasa jawabin, Archbishop Gallagher ya ce ya ziyarci Najeriya ne domin bikin cika shekara 50 da ƙulla hulɗar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Cocin Katolika, sannan ya ce Najeriya ƙasa ce mai matuƙar muhimmanci ga Cocin saboda yawan mabiya da kuma ƙarfinta.

    Ya kuma isar da godiyar Paparoma Leo XIV ga Shugaba Tinubu bisa halartar bikin rantsar da shi. Haka kuma ya bayyana jin daɗinsa da irin ci gaban da Jami'ar Veritas, wadda Cocin Katolika ta kafa a Abuja, ta samu.

  10. Waɗanda suka rasu a girgizar ƙasar Venezuela sun haura 3,000

    Gwamnatin Venezuela ta ce adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu sakamakon munanan girgizar ƙasar biyu da suka afku a ƙarshen watan da ya gabata a kasar sun kai kusan mutum dubu uku.

    Sai dai wata ƙididdigar da ba ta hukuma ba ta nuna cewa har yanzu sama da mutum dubu 40 ba a san inda suke ba.

    Wakiliyar BBC ta ce, masu aikin ceton gaggawa a arewacin Venezuela na ci gaba da aikin zakulo gawarwaki daga ƙarƙashin baraguzan gine-ginen da suka rushe, a yayin da ake ganin kusan babu sauran fatan gano waɗanda suka tsira.

    Shugaban Majalisar Dokokin Venezuela, Jorge Rodriguez, wanda kuma ɗan'uwan shugabar riƙon ƙwarya ƙasar ne, ya jaddada cewa ana ci gaba da ayyukan ceto a yankunan da bala'in ya shafa.

  11. Ranar Litinin za a zagaya da gawar Khamenei domin ban-kwana da ƴan ƙasar

    An ayyana yau Lahadi a matsayin ranar hutu ga daukacin al'ummar Iran ,a yayin da ake ci gaba da shirye shiryen jana'izar jagoran addinin ƙasar da ya rasu, Ayatullah Ali Khamenei.

    Ana sa ran gudanar da addu'oi a kan gawarsa da misalin ƙarfe shida na safe agogon GMT.

    Wakiliyar BBC ta ce a ranar Litinin ana tsammanin za a gudanar da babban taro inda za a zaga da akwatin gawarsa akan titunan birnin Tehran, kuma ana sa rana miliyoyin mutane za su fito domin bankwanda da gawar.

    Ana sa ran binne Ayatullah Ali Khamenei a garinsa na haihuwa, wato Mashhad, a ranar Alhamis.

    Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce Ayatollah Jafar Sobhani Tabrizi ne zai jagoranci addu'ar Khamenei da za a gudanar a harabar Mosalla da ke Tehran.

  12. Farawa

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da wannan safiya ta ranar Asabar.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.