Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 22/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Amurka tana saɓa alƙawuran tsagaita wuta - Pezeshkian

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce takunkumin da Amurka ke sanyawa kan tashoshin jiragen ruwan Iran, tare da barazana da kuma saba alƙawura, su ne suka haifar da babban cikas ga makomar tattaunawar da ake ƙoƙarin yi.

    Wakilin BBC ya ce irin wannan jan ƙafar da ake samu na ci gaba da haifar da shakku da fargaba game da yi yuwar tattaunawar da abin da za ta haifar.

    A wani rubutu da aka wallafa a shafukan sada zumunta, an zargi Amurka da yawan maganganu na shaci faɗi.

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar a ranar Talata cewa, ya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.

    Sai dai awanni kaɗan, rundunar Juyin juya halin Iran ɗin ta ce ta ƙwace wasu jiragen ruwa biyu, yayin da ƙasar ke ci gaba da sanya takunkumi kan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

  2. Rasha za ta dakatar da jigilar man Kazakhstan zuwa Jamus

    Rasha ta tabbatar da cewa za ta dakatar da jigilar man Kazakhstan zuwa Jamus ta bututun man da ya ratsa ta ƙasarta.

    Mataimakin Firaministan Rasha, Alexander Novak, ya ce za a dakatar da jigilar man ta bututun Druzhba daga farkon wata gobe, inda za a karkatar da shi zuwa wasu wurare na daban.

    Bayan da Jamus ta daina shigo da man Rasha sakamakon mamayar Ukraine, Kazakhstan ta zamo wacce ta maye gurbin wajen samar da Man.

    Mai magana da yawun gwamnatin Jamus, Stefan Kor-ne-lius, ya ce matakin na Moscow ba zai yi wani babban tasiri ba.

    Ya ƙara da cewa Berlin za ta ci gaba da sa ido kan samar da wadatacen man jiragen sama dake da mutuƙar mahimmanci.

  3. Trum ya ce Iran ta fasa zartar da hukuncin kisa kan mata 8 da aka kama yayin zanga-zanga

    Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa "An sanar da ni cewa Iran ta fasa zartar da hukuncin kisa kan mata 8 da aka kama saboda zanga-zanga"

    Shugaban ya ƙara da cewa: "Za a saki huɗu daga cikinsu nan take, yayin da aka yanke hukuncin zaman kaso na wata guda ga sauran huɗun."

    Trump ya ce yana godiya ga Iran da shugabanninta saboda mutunta roƙonsa a matsayin shugaban Amurka, lamarin da ya sa aka fara wannan hukuncin.

    A jiya ne shugaba Trump ya wallafa wani saƙo da yake roƙon Iran ta dakatar da hukuncin da ta yi niyyar zartarwa kan mata 8 ɗin, inda ya wallafa hotunansu.

    Sai dai Iran ta mayar da martani, inda ta ce shugaban na Amurka na amfani ne da labaran ƙanzon kurege, kuma babu wasu mata 8 da aka yanke wa hukuncin kisa.

  4. Ba za mu sake bude Hormuz ba duba da yadda aka keta yarjejeniyar tsagaita wuta - Iran

    Babban mai shiga tsakani na Iran da ke tattaunawa da Amurka, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce ba zai yiwu a sake bude mashigar Hormuz ba, duba da yadda aka keta yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta.

    Waɗannan “karya dokokin” sun hada da toshe jiragen ruwan Iran da Amurka ta yi - abin da ya ce ya jefa tattalin arzikin duniya cikin halin ƙaka-ni-ƙayi - da kuma “zafafa yaƙi” da Isra’ila ta ke yi “ta kowane ɓangare”.

    A martaninsa kan Amurka da Isra'ila, Ghalibaf ya bayyana a shafinsa na X cewa "ba su cimma burinsu ta hanyar ƙarfin soji ba, kuma ba za su cimma hakan ta hanyar cin zarafi ba.

    "Mafita ɗaya ita ce su mutunta ƴancin al'ummar Iran"

    Ana hasashen Gahlibaf zai tattauna da mataimakin shugaban Amurka JD Vance a Pakistan a wannan makon - amma har yanzu ba a fara ba.

    A daren jiya ne Donald Trump ya sanar da tsawaita wa'adin tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran da zai ƙare a yau.

    A safiyar yau ne Iran ta ce ta kame wasu jiragen ruwa guda biyu da ke dakon kaya a mashigar Hormuz.

  5. Mai yiyuwa a tattauna da Iran nan da ranar Juma'a - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce za akwai yiwuwar a fara zagaye na biyu na tattaunawar sulhu da Iran nan da ranar Juma'a, in ji jaridar New York Post.

    Jaridar ta ambato wani jami'an Pakistan na cewa mai yiyuwa ne a yi tattaunawar "a cikin nan da sa'o'i 36 zuwa 72 masu zuwa."

    Da jaridar ta tambayi Trump game da batun ya ce: "Akwai yiwuwar hakan".

    Ya ce za a ƙara wa'adin tsagaita wutar da aka cimma da Iran, wanda wa'adinsa zai ƙara a yammacin Laraba, domin ba gwamnatin Iran ƙarin lokaci domin gabatar da buƙatunta na da dakatar da yaƙin.

  6. Hungary ta janye ƙin amincewarta ga rancen dala biliyan ɗari da za a bai wa Ukraine

    Jakadun ƙasashen Tarayyar Turai sun amince da rancen dala biliyan ɗari da aka yi alkawarin bai wa Ukraine, bayan da Hungary ta janye ƙin amincewarta.

    Gwamnatin Mista Orban ta dakatar da amincewa da rancen ne a lokacin da Hungary ta daina karɓar man fetur daga Rasha ta bututun Druzhba, wanda ya ratsa cikin Ukraine, sakamakon takaddama da ta ke da Kyiv.

    Kyiv ta ce bututun ya lalace ne bayan wani harin Rasha, amma yanzu ya dawo aiki ka'in da na'in karon farko cikin watanni uku.

    Fira ministan mai barin gado Viktor Orban, ya zargi Kyiv da ƙin gyara bututun da gangan saboda dalilai irin na siyasa.

    Ana sa ran ƙasashen mambobin Tarayyar Turai za su kammala shirin amincewa da rancen a ranar Alhamis.

  7. Gomman mutane sun mutu sakamakon rikici tsakanin sojojin Ethiopia da ƴan ƙungiyar FANO

    Mutum bakwai sun mutu sakamakon wata arangama tsakanin dakarun gwamnatin Ethiopia da ƴan bindiga a yankin Amhara.

    Shaidun gani da ido sun ce dakarun gwamnati sun kai hari wata harabar coci a garin Sali a ranar Juma’ar da ta gabata.

    Mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin mafi muni, inda suka ce wasu daga cikin waɗanda aka kashe an tilasta musu durƙusawa kan gwiwoyin su kafin dakarun su buɗe musu wuta.

    Kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun zargi dakarun gwamnati da kuma mayakan na Fano da aikata kashe-kashe da sace mutane, tare da wasu nau’ikan cin zarafi.

  8. Ukraine ta fara tura mai ta bututun Druzhba zuwa Hungary da Slovakia

    Ukraine ta ce ta fara tura man Rasha ta bututun Druzhba zuwa kasashen Hungary da Slovakia a karon farko cikin watanni uku.

    An lalata bututun ne sakamakon wani harin jirgi mara matuƙi na Rasha a watan Janairun da ya gabata, kuma kasashen biyu -- wadanda suka dogara sosai kan man Rasha -- sun zargi Ukraine da gaza gyara shi da gangan.

    Kyiv ta musanta zargin.

    Yanzu haka dai Ukraine na fatan matakin zai buɗe hanyar samun rancen dala biliyan ɗari daga kungiyar EU wanda Firaministan Hungary mai barin gado Viktor Orban ya rike.

  9. An amince da sake fasalin gundumomin zaɓen jihar Virginia ta Amurka

    Masu zaɓe a Virginia ta Amurka sun amince da sake fasalin gundumomin zaɓen jihar, ta yadda sabon fasalin zai iya taimaka wa jam'iyyar Democrat samun nasarar iko da majalisar wakilan Amurka.

    Sabuwar taswirar za ta ƙara damar da jam'iyyar take da ita, ta samun karin kujeru huɗu a zaɓen da za a yi na rabin wa'adi a watan Nuwamba.

    Yan Democrat na buƙatar samun ƙarin kujeru 'yan kaɗan ne a faɗin Amurka, su kawar da ɗan rinjayen da 'yan Republiacn suke da shi a majalisar wakilan - wanda hakan zai ba 'yan Democrat din damar taka birki ga manufofin Shugaba Trump a majalisa.

    'Yan Democrat din jihar ta Virginia, sun ce sun yi hakan ne domin tabbatar da adalci a tsarin zabe, ta hanyar martani ga irin wannan tsarin da 'yan Republican suka yi a wasu jihohin na Amurkar.

  10. CBN ya ce ana ta yunƙurin yiwa 'yan Najeriya kutse a bankunansu

    Babban bankin Najeriya CBN ya gargaɗi 'yan ƙasar da su kasance cikin shiri saboda masu kutsen Intanet da ke ta yunƙurin kutse cikin asusun ɗaiɗaikun mutane.

    Babban bankin ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannun muƙaddashiyar harkokin watsa labarai Hakama Sidi Ali a ranar Talata.

    CBN ya ce masu kutse na tura wani saƙo na bogi zuwa ga email ko sakon karta kwana na mutane suna cewa daga bankin sakon yake.

    A cewa sanarwar akwai cutar da mutane a saƙon inda suke neman mutum ya danna wani link daga nan kuma sai su samu damar shiga cikin asusun.

    Daga nan kuma sai su bar me asusun da zargin CBN ya sace masa kudi.

  11. Yarjejeniyar tsagaita wutar Trump 'fanko ce'

    Wani babbban mai ba da shawara a Iran ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaban Amurka Donald Trump ya nemi a tsawaita 'fanko ce', yana cewa "wani salo ne na sake jan ƙafa kan tattaunawar gaba".

    Mahdi Mohammadi mai ba da shawara ne ga kakakin majalisar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mohammad ya ce ci gaba da yajejeniyar tsagaita wutar babu abin da ya rabata da lokacin da ake kai hare-hare" kuma dole a mayar masa da martani irin na soji, inda ya ƙara da cewa "Lokaci ya yi da Iran za ta fara nata shirin."

    Sojojin ruwan Amurka sun toshe tashoshin ruwan Iran tare da mashigar Hormuz.

  12. China ta rage farashin man fetur da dizal saboda yaƙin Iran

    China za ta rage farashin man fetur da dizal a karon farko tun bayan soma yakin Iran, domin ya yi dai dai da farashin mai a kasuwar duniya, a cewa hukumar kawo ci gaba da sauyi ta ƙasar.

    Hukumar, wadda ke tsara tattalin arzikin China, tana ƙayyade farashin man fetir duk bayan makonni biyu, bisa la'akari da farashin ɗanyan mai a duniya a lokacin.

    Rage farashin zai taimakawa masu ababen hawa samun ragin aƙalla dala uku a lokacin da za su siya lita hamsin na fetir ɗin.

    Beijing ta kara farashin man fetur da an dizel sau da dama tun soma yakin, wanda ya sa farashin yin tashin gwauron zabi.

  13. Jiragen Koriya ta Kudu sun yi hatsari lokacin da matuƙan ke ɗaukar hoto

    Wani bincike da aka gudanar a Koriya ta Kudu ya gano cewa wasu jiragen saman yaƙi biyu sun yi taho mu gama a sararin samaniya saboda matuƙan su na ta ɗaukan hotuna da bidiyo da wayoyinsu yayin da suke tuƙi.

    Lamarin ya faru ne shekaru biyar da suka gabata, a yayin da suke wani aiki a birnin Daegu.

    Masu binciken sun gano cewa ɗaya daga cikin matuƙa jirgin ya ce yana so ya dauki hotunan ranar sa ta ƙarshe yana tuƙa jirgi da sashen da yake aiki a lokacin.

    Shi kuwa matuƙin ɗayan jirgin bidiyo yake yi.

    Daga bisani jiragen samfurin F-15k suka yi karo, duk da dai basu kai ga faɗowa ƙasa ba.

    Gyara jirgin ya laƙume fiye da dala dubu ɗari huɗu.

  14. Fatan sake tattaunawar zaman lafiya a Pakistan na fuskantar cikas

    Donald Trump ya yi iƙirarin kawo sauyi a Tehran sai dai ya zuwa yanzu yana fama ne da abin da ya kira rashin fasalin gwamnati.

    Yanzu da manyan shugabannin Iran suka mutu, tambayar da aka gaza masun amsa ita ce wane ne yake mulki yanzu, hakan dai yana rikita matakin diplomasiyya na wanda za a rika magana da shi.

    A 'yan bayan nan za ka iya cewa matakinsa ya yi nasara shi Trump sai dai wanda zai tabbatar da abin da yake nema daga Tehran shi ne zai yi wuya.

    Mai baiwa kakakin Majalisar Iran shawara da ke jan ragamar tattaunawar Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce ana jiran wani lokaci ne kawai da za sake kai harin ban mamaki.

    Wani sojan Amurka ya yi gargaɗin cewa Iran za ta ira kai hari da wani abu makamancin haka ya faru.

  15. An samu wani ɗan China da cutar Corona a Najeriya

    Ma'aikatar lafiya ta jihar Cross River da ke kudu maso kudancin Najeriya ta tabbatar da samun mai ɗauke da cutar Corona a jihar.

    Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Henry Ayuk, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce an tabbatar da hakan ne a ranar 17 ga watan Afrilun 2026, kuma wani ɗan China da ya shigo ƙasar ranar 17 ga watan Maris ne ke ɗauke da cutar.

    Ya ce jikin mara lafiyan ya yi tsanani ne a lokacin da ya ke wani asibiti da ke karkashin ofishin da ya ke aiki, kafin daga bisani aka garzaya da shi asibitin koyarwa na jami'ar Calabar.

    A cewarsa bayan yi masa gwaje gwaje a asibitin ne aka tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar, kuma a yanzu haka an killace shi.

    Ya kuma buƙaci yan jihar da kar su tayar da hankalinsu, a cewarsa suna duk mai yiwuwa na hana cutar yaɗuwa, da ma duk wata cuta a jihar.

    Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da lamarin, kuma ta ce tana aiki da gwamnatin jihar domin shawo kan lamarin.

  16. Iran ta kai hari kan wasu jiragen ruwa a Mashigar Hormuz

    Dakarun Iran sun kai hari kan wani jirgin dakon kaya mallakin Girka a Mashigar Hormuz.

    Bisa bayanan da BBC ta gani, an gano cewa jirgin Epaminondas ne.

    Tun da farko an bayyana wa matuƙin jirgin cewa yana da izinin wucewa.

    Amma daga bisani wani jirgin ruwa yaƙin dakarun juyin juya halin Iran ya buɗe masa wuta.

    A gefe guda kuma wata hukumar kula da sufurin jiragen ruwa na Birtaniya (UKMTO) ta ruwaito cewa an buɗe wuta kan jirgin na biyu a mashigar.

    Jirgin dakon kayan na ƙoƙarin barin yankin ne a lokacin da aka kai masa hari, a yanzu kuma ana tsare da shi kan ruwan.

    Rahotanni sun ce jami'an jirgin na cikin ƙoshin lafiya.

  17. Sojojin hayan Colombia masu samun goyon bayan Haɗaddiyar daular Larabawa na taimaka wa RSF - Rahoto

    Wani sabon rahoto ya nuna cewa sojojin haya na Colombia da ke samun goyon bayan Haɗaddiyar daular Larabawa sun taimaka wa dakarun kungiyar RSF ta Sudan sake kama birnin el-Fasher na Sudan a shekarar da ta wuce.

    Babban mai binciken ya ce wannan ne bincike na farko da ya tabbatar da cewa Hadaddiyar daular Larabawa tana da alaka da kungiyar ta RSF, ba tare da wata tantama ba.

    Wakiliyar BBC ta ce kungiyar ta ce bayanan sun nuna alaka na daban-daban da Hadaddiyar Daular Larabawar.

    Kungiyar da ta yi binciken - Critical Insights Group, ta ce Hadaddiyar daular Larabawa da sojojin na Colombia na da alhakin laifukan azabtarwa da dakarun RSF suka yi a lokacin sake kwace birnin, wanda yana daya daga cikin mummunar ta'asa da aka yi a yaƙin basasar na Sudan.

    Har kullum dai Hadaddiyar daular na musanta taimaka wa RSF.

  18. Gwamnan Kano ya zaɓi Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakinsa

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya aika sunan Murtala Sule Garo domin neman amincewa da shi a matsayin sabon mataimakinsa.

    A cikin wata sanarwa da babban jami'in yaɗa labarai na gwamnan Mustapha Muhammad ya fitar, ya ce bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, Gwamnan ya buƙaci majalisar dokokin jihar ta amince da naɗin Garo.

    Sanarwar ta kuma ce Gwamnan ya gabatar da sunansa ne a ƙoƙarin gwamnatin na karfafar aikin gwamnatin da kuma inganta gudanar da ayyuka a jihar ta Kano.

    Wannan na zuwa ne bayan da tsohon mataimakin gwamnan Kwamared Abdulsalam Gwarzo ya yi murabus a baya bayan nan.

    Ana ganin Gwarzo ya ajiye aikin ne bayan ƙin amincewa ya bi gwamnan jihar zuwa jamiyyar APC bayan ficewa daga NNPP duk da shan matsi.

  19. MDD ta yi maraba da tsawaita dakatar da buɗe wuta a Iran da Amurka ta yi

    Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi maraba da sanarwar da Shugaba Trump ya yi ta tsawaita dakatar da buɗe wuta da Iran har sai an kammala tattaunawa.

    Mai magana da yawun Antonio Guterres, ya bayyana hakan a matsayin mataki mai alfanu, da zai bayar da damar samun maslahar diflomasiyya.

    A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta Trump ya yi gargadin cewa, Amurka za ta ci gaba da toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran, har sai Iran ɗin ta gabatar da abin da ya kira matsayi na bai ɗaya a kan tattaunawar.

    Wakiliyar BBC ta ce duk tsawon lokacin wannan rikici Trump na amfani da shafin sada zumunta da sanarwa a talabijin ya yi gargadi ga Iran.

    Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif wanda ke shiryawa da karɓar baƙucin tattaunawar ya ce yana fatan ɓangarorin biyu za su ci gaba da mutunta dakatar da buɗe wutar.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar yau Laraba.

    Yau ma kamar kullum mun dawo muku da shafin namu na kai tsaye inda muke kawo muku muhimman labarai dangane da al'amuran yau da kullum, musamman kan yakin Iran da Amurka da kuma kan Najeriya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa kamar Facebook, Instagram, X, da kuma YouTube.