Nan muka kawo karshen shirin
Da fatan za ku tara a daya wasan daf da karshe a ranar Laraba tsakanin Ingila da Argentina.
Wa zai hadu da Sifaniya a wasan karshe?
Sunana Mohammed Abdu nake ce muku asuba ta gari.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Abdu tare da taimakon AI
Da fatan za ku tara a daya wasan daf da karshe a ranar Laraba tsakanin Ingila da Argentina.
Wa zai hadu da Sifaniya a wasan karshe?
Sunana Mohammed Abdu nake ce muku asuba ta gari.
Za mu kawo muku kai tsaye wasan Ingila da Argentina a ranar Laraba.
Duk wadda ta yi nasara za ta fuskanci Sifaniya a wasan karshe ranar Lahadi.
Duk wadda aka ci kuwa za ta fafata da Faransa a ranar Asabar a neman mataki na uku.
An tashi wasan kuma Sifaniya ta kai wasan karshe da za a buga ranar Lahadi.
A gobe ne za a buga daya wasan daf da karshe tsakanin Ingila da Argentina
Sifaniya na rike kwallon tana bani in baka, saboda kada Faransa ta samu dama, kuma kwallo daya ne ya ciga ragar Sifaniya kawo yanzu ta zura kwallo 13 a raga.
Mbappe ya samu bugun tazara daf da gidan Sifaniya, sai dai kwallon da ya buga ta yi sama da yawa ta fita waje.
Kylian Mbappe ya yi satar gida har karo uku fiye da kowanne dan wasa a karawar nan.
Sau daya ya buga kwallo ta nufi raga ya kwaci kwallo sau biyu daga takwas da aka yi gwagwar maya.
Duk da yake Kylian Mbappe da Ousmane Dembele har yanzu suna cikin fili, wannan wasan bai ƙare ba tukuna. Faransa na buƙatar waɗannan biyun su yi wani abu na musamman kuma su yi shi yanzu.
A cikin duk hasashen da aka yi kafin wasan nan, ƴan kalilan ne za su yi la'akari da wannan wasan ya riga ya yi nisa.
Roy Keane, tsohon kyaftin din Jamhuriyar Ireland a ITV
"Ba zan yi matukar sukar Faransa ba saboda tawaga ce mai kyau amma ba sa wasa a matsayin da ya kamata. Tabbas, tawagar Spain tana da kyau.
Canji biyu ga Faransa yayin da Rayan Cherki na Manchester City ya canji Michael Olise, Theo Hernandez shima ya maye gurbin Lucas Digne.
Minti 75 da suka gabata kuma Faransa ta kasa kai hari ko sau daya, kenan yadda aka rufe Faransa a wasan nan.
Ga yadda Lamine Yamal ya kasance a satar gida da tuni wasan yana 3-0.
Da tuni mun tabbatar da Sifaniya zuwa wasan karshe. Amma yanzu da saura lokaci.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana a kan babban allo a cikin filin wasa, sai wani sashen yan kallo ya yi masa ihu, shi kuma sai ya yi murmushi.
Za kuma su dawo a karasa karawar da Sifaniya ta ci Faransa 2-0.
Da Alama Sifaniya ce za ta kai wasan karshe, sai a kwallon kafa komai zai iya faruwa.
Kawo yanzu an rufe Mbappe bai samu irin damar da yake bukata ba.
Kenan kafar Faransa za ta tsaya buga wasan neman mataki na uku, yayin da Sifaniya za ta je wasan karshe idan aka tashi haka.
Lamine Yamal ne ya samu ya zura a raga, amma an soke da cewar an yi satar gida,
Kwallo ce mai kyau aka ci Faransa, inda Porro ya bai wa Dani Olmo, shi kuma dan baya na jikinsa sai ya taba ta gefe nan da nan Porro ya kara gudu ya yi gaba da gaba da mai tsaron raga ya buga gefe da karfi ta fada raga.