Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Hezbollah ke amfani da jiragen sama marasa matuƙa wajen kai wa Isra'ila hari
- Marubuci, Luke Unger and Adam Durbin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Hezbollah ta ƙara yawan harin jiragen sama marasa matuƙa da ta ke kai wa Isra'ila, cikin harda sabbin jiragen zamani masu amfani da fasahar fasa na'urar kare sararin samaniya.
Sashin tantance lanarai na BBC Verify ya yi amfani da na'urar tantance ingancin bidiyo domin gano gaskiyar wasu bidiyo 35 da dakarun Lebanon suka wallafa daga ranar 26 ga watan Maris, waɗanda suka nuna hare-haren su a kan sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon.
Ƙwararru sun shaidawa BBC Verify cewa ƙananan jiragen sama marasa matuƙi da Hezbollah ke harbawa na keta na'urar kare sararin samaniyan Isra'ila, tare da aikata ɓarna kan dakarun Isra'ilan.
Ƙwararrun sun kuma ce ƙananan jiragen ba su da tsadar ƙerawa, idan aka kamanta su da mummunar ɓarnar da suke yi idan aka harba su.
A yaƙin Rasha da Ukraine ne amfani da irin waɗannan ƙananan jirage masu saukin kuɗi ya yawaita, kuma hakan ya canza dabarun yaƙi na zamani da ake bi.
Duk da cewa dakarun sojin Ira'ila ba su fitar da cikakken bayaninɓarnar da ake masu ba, kafafen yaɗa labarai a ƙasar sun ruwaito cewa an kashe dakarun Ira'ila huɗu da farar hula ɗaya bayan raunata wasu gommai, a hare-haren jiragen sama marasa matuƙi
Rundunar sojin Ira'ila ta shaidawa BBC Verify cewa tana sane da barazanar da jirage marasa matuƙin ke yi don haka take ware ''kasafi mai tsoka'' ga aikin inganta na'urar kare sararin samaniyar ta domin tafiya daidai da zamani da kuma ƙara bayar da horon aiki na zamani ga dakarun su.
Cibiyar koyar da tsaron ƙasa ta ce itama rundunar sojin Isra'ila tana amfani da ƙananan jiragen sama marasa matuƙan da ake kira FPV tsawon shekarau, kuma ko a baya-bayan nan ta yi amfani da su a kudancin Lebanon da kuma Gaza.
Hisham Jaber, wani tsohon janar ɗin sojin Lebanon kuma mai sharhi kan harkokin tsaro ya shaidawa sashin Larabci na BBC cewa jiragen na FPV suna yi wa na'urar kare sararin samaniya sammatsi ta yadda ba a iya ganin su, kuma ya tabbatar da cewa Hezbollah ta mallki ''ɗaruruwan su'' inda ake amfani da su wajen kai hari a kan tankokin yaƙi.
Jaber ya ƙara da cewa Hezbollah ta daɗe tana amfani da waɗannan jirage wajen kai hare-hare a arewacin Isra'ila amma ''a yanzu da suke ɓullo da sabon salon amfani da jiragen na zamani'' da alama sun fi na da haɗari.
BBC Verify ya ga bidiyo aƙalla 100 na amfani da jiragen FPV wajen kai hare-hare, waɗanda Hezbolah ta wallafa a shafin Telegram tun daga 26 ga watan Maris, kuma ta tantance 35 daga cikin su.Hezbollah ba ta wallafa irin waɗannan bidiyo ba a farkon yaƙin, a ranar 2 ga watan Maris.
Wani bidiyo da aka wallafa a ranar Alhamis ya nuna aƙalla jiragen FPV huɗu suna kai hari a kan iyakar Isra'ila kusa da Kiryat Shmona, inda suka harba makamai kan wasu motocin sojin Isra'ila. Bidiyon ya nuna aƙalla motoci biyu da harin ya lalata.
BBC Verify ya kuma tantance wasu hare-hare masu kama da wannan a kudancin Lebanon, ciki harda biyu da aka kai a ranar 26 ga watan Afirelu a garin Taybeh. Bidiyon sun nuna yadda aka kai hari a kan sojoji da kuma wani da aka kai a kan jirgin sama mai saukar ungulu mallakin rundunar sojin Ira'ila, a daidai lokacin da yake ƙoƙarin kai ɗauki ga dakarun da suka samu rauni. Kafar yada labaran Isra'ila ta ruwaito cewa an kashe soja ɗaya tare da raunata wasu shida.
Mafi yawan jiragen nan suna amfani da ƙololuwar fasahar zamani ta yadda ba su buƙatar irin kayan aikin da sauran jiragen da aka sani ke amfani da su, lamarin da ya sa da wuya a iya tare su a lokacin da suke kai hari.
Dr Andreas Krieg, masanin tsaro a King's College da ke birnin Landan, ya shaidawa BBC Verify cewa ƙololuwar fasahar da jiragen ke amfani da ita ta sa rundunar sojin Isra'ila ba ta iya gano su ko kuma hana su kai hari.
Ya saboda haka dole dakarun Isra'ila suka koma yin taka tsantsan wajen zirga-zirga , da kuma amfani da manyan kayan bayar da kariya ga motocin su a duk lokacin da suke tafiya.
Krieg ya ƙara da cewa Hezbollah tana haɗa waɗannan jiragen ne a cikin gida duk da dai akwai wasu kayayyaki da take saye daga China domin haɗa su, kuma farashin su yana kamawa ne daga $300 zuwa $500 (£225-£375) kowanne ɗaya.
Faɗan baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da Hezbollah ya ɓalle ne a ranar 2 ga watan Maris, kwana biyu bayan Amurka da Isra'ila sun kai hare-hare cikin Iran, inda suka kashe jagoran addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei.
Bayan mutuwar Khamenei, Hezbollah ta harba makaman roka cikin Isra'ila, inda itama Isra'ilan ta mayar da martani da hare-haren sama a Lebanon da kuma na ƙasa a kudancin ƙasar.
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce mutane aƙalla 2,896 aka kashe tun daga lokacin, ciki harda wasu fiye da 400 tun bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta a watan Afirelu. Ma'aikatar ta ce ƙididdigar ba ta rarrabe tsakanin sojoji da fararen hula ba a cikin mutanen da aka kashe.
Mutane fiye da miliya ɗaya aka tilastawa barin muhallin su tun bayan fara yaƙin a Lebanon.
Isra'ila ta ce an kashe mata soja ɗaya da fararen hula 18 a yaƙin.
Additional reporting by Ƙarin rahoto daga Lamees Altalebi da Thomas Spencer da Deena Easa da Sherie Ryder da Paul Brown da kuma Tom Shiel.