Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me cutar Ebola ke yi wa jikin wanda ta kama?
Cutar Ebola ta sake tayar da hankalin jama'a a Najeriya bayan da gwamnatin ƙasar ta tabbatar da ɓullar cutar a Abuja, babban birnin ƙasar.
Ministan lafiyar kasar, Farfesa Ali Pate, ya ce wata mata ce ta kawo cutar bayan komawarta ƙasar daga Uganda a jirgin sama, kuma an killace ta tare da fara bibiyar mutanen da suka yi mu'amala da ita domin daƙile yiwuwar yaɗuwar cutar.
Wannan sanarwa ta zo ne shekaru 12 bayan Najeriya ta yi nasarar shawo kan ɓarkewar Ebola da ta afku a shekarar 2014, wadda ta jawo ɗimbin damuwa a cikin ƙasa da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.
A yanzu hukumomi na cewa sun gano mutum 44 da suka yi mu'amala da matar, yayin da aka sanya cibiyoyin lafiya cikin shirin ko-ta-kwana.
Ebola na daga cikin cututtuka masu haɗari da ke haddasa zazzaɓi mai tsanani kuma tana iya kai wa ga lalacewar wasu muhimman gaɓoɓin jiki.
Yaya cutar ke yaɗuwa?
Dr Nasir Sani Gwarzo, ƙwararren likita kan cuta masu yaɗuwa a Najeriya, ya ce cutar Ebola kan kwashe fiye da mako guda a jikin wanda ya kamu da ita kafin ta fara nuna alamomi.
''Saboda da haka duk wanda ya yi mu'amala da mai ɗauke da cutar a lokacin da yake kan ganiyar cutar to zai iya kamuwa da ita'', in ji shi.
Don haka ne ya bayar da shawarar cewa a duk lokacin da aka samu labarin cewa wani ya yi mu'alama da mai cutar ko ya ce ƙasar da ake yin cutar to abin da ya kamata shi a a killace shi.
''Daga ranar da mutum ya samu cutar, daga lokacin ne zai fara yaɗa ta'', in ji shi.
Ya ce ana iya yaɗa cutar ta hanyoyin da suka haɗa da:
- Gumi/Zufa
- Yawu
- Hawaye
- Fitsari
- Amai da gudawa
- Fatar jikinsa
- Tufafin mai ɗauke da cutar
Likitan ya ce duk ani abu mai danshi da ke fita a jikin mutum idan wani ya taɓa zia iya kamuwa da cutar.
''Haka kuma za a iya ɗaukar cutar ta hanyar taɓa gawar mutumin da ya ta mutu sakamakon cutar'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa ba a ɗaukar cutar Ebola ta hanyar iska, ko numfashi.
Mene ne alamominta?
Ƙwararren likitan ya bayyana wasu alamomi da ya ce da su ne ake iya gane mai ɗauke da cutar da suka haɗa da:
- Zazzaɓi mai tsanani
- Zazzaɓi mai kama da maleriya
- Amai da gudawa
- Mura
- Fitar da jini
- Ciwon kai
- Kasala
- Ciwon jiki
Waɗanne illoli take yi wa waɗanda ta kama?
Masanin lafiyar ya ce cutar da Ebola na yi wa wanda ta kama mummunar illa ga jikinsa.
''Na farko zazzaɓin Ebola mummunan zazzaɓi ne da ke yin tasiri a jikin wanda ta kama, ko da mutum ya warke idan ka gan shi sai ka tausaya masa'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa cutar kan narkar da ƙwaƙwalwar mutumin da ta kama.
''Wanda ta kama ko da ya warke sai ka ga alama a jikinsa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya ce idan ka ga zazzaɓin wanda ya kamu da Ebola, ''ba za ka so ka sake ganinsa ba, saboda mummunan halin da yake shiga''.
Yadda za ku kauce wa kamuwa da cutar?
Dr Gwarzo ya lissafo matakan da ya kamata mutane su bi domin kauce wa kamuwa da wannan cuta.
''Na farko shi ne mutum ya samu ilimin yadda zai kula da kansa a lokacin cutar'', in ji shi.
Likitan ya kuma bayar da shawarar kauce wa shiga cunkuson jama'a.
''A yawaita wanke hannu sosai da sabulu'', in ji shi.
Game da hukumomi kuwa Dr Gwarzo ya ce yana da kyau gwamnatocin jihohi su ɗauki matakamn gaggawa na kare yaɗuwar cutar tun kafin ta bayyana ajihohinsu.